Tun a daren jiya ne dai Kakakin Kwamitin Tsaro a majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Dr. Ibrahim Riza’i, ya bayyana cewa; Iran za ta mayar da martani akan harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai wa unguwar Dhahiya a cikin birnin Beirut, wanda kuma zai kasance mai tsanani.
Ibrahim Riza’i ya kuma kara da cewa; Wajibi ne a ladabtar da wannan mahaukacin karen mai haaushi, da zaunar da shi daidai da matsayarsa.
Ibrahim Riza’i ya kuma kara da cewa; Idanuwanku su koma sararin samaniyar haramtacciyar kasar Isra’ila domin ganin abinda zai faru.
A gefa daya, mai bai wa jagoran juyin musulunci shawara Muhammad Mukhbari ya ce; Makiya sun sake kunna wutar yaki a daidai lokacin da ake kan ganiyar tattaunawa ta hanyar kai hari a Beirut, don haka za su dandanta kudarsu.
Muhammad Mukhbari ya kara da cewa; Kawancen gwgawarmaya tamkar gangar jiki ne guda daya, don haka wadanda su ka kai harin a Beiruta za su dandana kudarsu.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto mai bai wa jagoran juyin shawara yana cewa; Da harshen karfi muke magana da wadanda su ka saba karya alkawali, don haka za su dandana kudarsu akan wannan haarin da su ka kai a lokacin da mai shiga tsakani ya zo Iran.
.