Hukumar zaben Chadi ta sanar da nasarar Mohamed Idriss Deby a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa
Hukumar zabe ta gwamnati a kasar Chadi a jiya Alhamis ta fitar da sanarwar cewa: Shugaban kasar na rikon kwarya Mohamed Idriss Deby ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu a zagayen farko na zaben bayan ya samu kashi 61% na kuri’un da aka kada.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan adawa suka yi zargin tafka magudi a zaben, kuma fira ministan kasar kuma dan takarar babbar jam’iyyar adawa Sukseh Masra a gabanin fitar da sakamakon zaben, ya bayyana nasararsa a zaben shugaban kasar a wani sako kai tsaye da aka watsa ta kafar Facebook.