Search
Close this search box.

 HKI Ta Rufe Ofisoshin Jakadancinta 5 A Duniya Saboda Tsoron Mayar Da Martani Daga Iran

Jaridar Bedioy Ahranot ta buga labarin dake cewa;  ofisoshin jakadancin da aka rufe su ne na kasashen  Bahrain, Masar, Jordan, Moroko da Turkiya. HKI ta

Jaridar Bedioy Ahranot ta buga labarin dake cewa;  ofisoshin jakadancin da aka rufe su ne na kasashen  Bahrain, Masar, Jordan, Moroko da Turkiya.

HKI ta dauki wannan matakin ne bayan harin ta’addancin da ta kai wa karamin ofishin jakadancin Jamhuriyar musulunci ta Iran dake birnin Damascuss na kasar Syria.

A sanadiyyar wancan hari na ranar Litinin, janar Muhammad Riza Zahidi, Muhammad Hadi-Haji Rahimi, tare da wasu mutane 5 da suke tare da su, sun yi shahada.

Kasashe da dama ne na wannan yankin da kuma duniya su ka yi Allawadai da harin na ‘yan sahayoniya wanda yake a matsayin take dokokin kasa da kasa.

Bugu da kari, wasu majiyoyin ‘yan sahayoniyar sun ambaci cewa; sojoji suna cikin shirin ko-ta-kwana saboda mayar da martani akan abinda zai iya faruwa.

Jamhuriyar musulunci ta Iran dai ta sha alwashin daukar fansar harin da ‘yan sahayoniyar su ka kai wa  karamin ofishin jakadancin nata dake Damascuss, tare da kashe mata manyan sojoji.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments