Tsohon Mai Bawa Shugaban Kasar Amurka Shawara Ya Ce Isra’ila Ce Ta Jawowa Kasar Mummunan Halin da Take Ciki
Tsohon mai bawa shugaban kasar Amurka shawara na musamman Steve Bannon ya bayyana cewa, kasancewar Amurka bayan Isra’ila ne ya jawo wa jam’iyyar republican faduwa a zaben rabin wa’adi na 3 ga watan Nuwamban da muke ciki.
Tashar talabijan ta Almayadeen tv ta kasar Lebanon ta nakalto Steve Bannon yana fadar haka a lokacinda yake hira da Jaridar TELEGRAM na Amurka, ya kuma kara da cewa, shi baya goyon bayan shi’arin ‘Isra’ila a fasko’. Kuma da shugaban Trump takaita da ruwan boma boman da yayiwa cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran a watan yunin shekara ta 2025 ya yafi masa, da kuma bamu fada cikin halin da muke ciki ba, kuma da Jam’iyyar Republican bata sha irin wannan mummunan kaye da ta sha saboda yakin da ta shiga da Iran ba.
Bannon dai ya kasance mai bawa shugaban kasar Amurka Donal Trump Shawara kan al-amura na musamman a zagayen shugabancinsa na farko. Kuma yana tare da shi a lokacinda Amurka da HKI suka farwa kasar Iran da yaki a karo na farko ashekara ta 2025 na tsawon kwanaki 12.
Ya ce: Biyan bukatar haramtacciyar kasar Isra’ila ce ya jawowa Amurka faduwa a gaban Iran wanda asarar da aka yi saboda hakan ba zai misaltu ba.