Aya. Sheikh Isa Qasim, shugaban masu gwagwarmaya da sarakunan Alee Khalifa azzzalumai, ya bayyana cewa, hukuncin daurin rai da rai wanda gwamnatin Bahrain ta yankewa malaman addini 60 a kasar ya nuna cewa, sun kasa tursasawa mutanen kasar su zama bayin sarakunan kasar ba.
Tashar talabijan ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto Aya. Qasim yana fadar haka a jiya Litinin ya kuma kara da cewwa, mutanen kasar Bahrain ba zasu taba zama bayin Aali Khalifa ba.
Ya ce duk wata kasa wacce mutanen kasar suke son yenci kuma basa son bauta to kuwa dole a daure maloamansu a kuma yanke masu hkuncin da aka yanke. Y ace rayuwarsu shi ne musulunci da jihadi kan tafarkin addinimmu da kuma diyaucimmu. Dauri ba zai taba girgizamu ba, kuma ba zai taba hana mu neman yencimmu ba.
Kafin haka dai wata kotu a kasar Bahrain ta yanke hukuncin daurin rai da rai na mutane 69 kuma dukkaninsu mabiya mazhabar iyalan gidan manzon All..(s), 60 daga cikinsu malaman adddinin sannan mutane 5 daga cikinsu daurin shekaru 15 a gidan kaso.
Banda haka kotun ta yanke hukunci kan wasu 13 wadanda basahannu daga ciki har da shugabansu Aya. Isa Qasim wanda yake gudun hijira a birnin Qom na kasar Iran.