Wasu kasashen Tarayyar Turai biyar sun amince da wani tsari da zai bayar da damar samar da wani sansanin jibge bakin haure a kasar Rwanda, da zai shafi mutanen da ke samun mafaka a kasashensu ba tare da cikakkun takardun izini ba, matakin da ya jima yana fuskantar suka, musamman daga kungiyoyin kare hakkin Ɗan Adam.
Kasashen biyar sun hada da Jamus, da Austria da Netherlands, Denmark da Greece, kuma sun ce wannan sabon aikin kwashewa da jibge bakin hauren zai shafi iya wadanda suka gaza samun damar hakan a gaban kotu ne.
A wata sanarwar hadin gwiwar da kasashen suka fitar, sun ce kwakkwarar yarjejeniya da suka cimma da Rwanda zata fara aiki nan take, kuma kasashen ne zasu hada kudaden kwashe mutanen da kuma kai su kasar ta gabashin Afrika.
Gwamnatocin kasashen na fatan tasa keyar mutane akalla 100 zuwa Rwanda a kason farko, a farkon shekara mai kamawa don yin gwajin shirin. karkashin tsarin za’a baiwa mutanen da aka mayar Rwanda damar zabar ci gaba da zama a kasar ko kuma komawa kasashensu na asali bayan yan watanni da isa.
.