Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran reshen kula da sararin samania sun sami nasarar sauke wani jirgin yakin Amurka samfurin MQM-170 a kudancin tsibirin Qeshm na tekun Farisa a jiya litinin bayan da kwarraru suka kwace ikon sarrafa Jirgin suka kuma sauke shi a kan ba tare da ya lalace ba.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar IRGC na cewa wannan shi ne jirgin Drone na Amurka samfurin MQM-170 na 9 da suka sauke ba tare da kakkabosu ko kuma lalatasu ba.
Majayar ta bayyana cewa, wannan ya nun a cewa kwamandojin dakarun Amurka CENCOM suna kasa sarrafa jirgin idan ya isa sararin samaniyar JMI. Wanda kuma ci bayane sosai cikin rundunar ta Amurka.
Dakarun IRGC reshen kula da sararin samaniyar JMI, kuma masu fafata yakin na’urorin lantar da Amurka, tare da dogaro da kayakin aiki da horawa na cikin gida, sun nuna kwarewarsu fiya da tokwarorinsu na Amurka a fanan fannin. Tunda ya tabbata cewa ba zasu iya kare kayakin aikinsu daga nesa ba.