rahotanni sun bayyana cewa wata mata bafalasdiniya ta mutu sakamakon harin da wani gungun yahudawa yan share wuri zauna suka kai inda suka rika harbin falasdinawa da harsashi mai rai a kauyen Duyuk al-tahta dake yammacin ariha a bagar yammacin kogin jodan da isra’ila ta mamaye
kamfanin dillancin labaran wafa na yankin falasdinu ya bayyana cewa bincike da aka gudanar ya tabbatar da mutuwar matar yar shekaru 60 da haihuwa mai suna Fadwa mohammad fahidat, kamar yadda darakatan asibitin ariha na gwamnati ya tabbatar cewa wata mata ta mutu da aka harbe a kai.
mahukumtan isra’ila sun bayyana cewa suna gudanar da bincike kan rahoton da aka watsa na yunkurin kai hari a ariha, kuma sojojin sun isa wajen da kuma kafa shingayen bincike
ma’aikatar harkokin wajen falasdinu tayi tir da matakin da sojojin isra’ila suka dauka inda suka afkawa wani gari kana suka rufe babar hanya da hakan ya hadda cunkosun ababen hawa, kuma ta dora alhakin hakan kan isra’ila, yadda take bada kariya ga yan share wuri zauna suna kai hari kan falasdinawa