Iran Tayi Tir Da Hukumcin Da Aka Yankewa Malaman Shia A Bahrain

kasar iran ta yi suka game da hukumcin da gwamnatin bahrain ta yanke kan wasu malaman shia na zaman gidan yari har abada

Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta yi tir da hukunci mai tsanani da gwamnatin kasar baharain ta yanke na daurin rai da rai kan wasu manyan malaman shi’a yan kasar, bisa zarge-zarge marasa tushe balle madafa, kuma ta bayyana matakin a matsayin take hakkin bil adama

Ma’aikatar ta fitar da wannan bayanin ne a yau talata ,inda tace yanke hukuncin zama gidan yari har abada kan malaman addini , yazo ne bayan kalaman batanci  da sakataren wajen amurka ya yi kan malamai da fitattun mutane yan shia, wanda hakan ya nuna irin yadda mahukumtan kasar Bahrain sun kayi daidai da matakin da gwamnatin amurka ta dauka na haifar da fitinar bangaranci

Babbar kotun kasar Baharain ta yanke hukumcin kan babban malamin shia na kasar Ayatullah shaikh isa Qaseem da sauran malamai 63 da sauran wasu yan adawa na zama a gidan yari har abada, da kuma zaman shekaru 15 ga wasu malaman

Idan ana iya tunawa a ranar jumaa da ta gabata sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubio yayi ikirarin cewa malam shi’a a iran suna da hannu wajen matsalolin dake faruwa a yammacin asiya, duk inda aka duba akwai wani abu da ya zama na gama gari, malaman shi’a na iran da kuma manufofinsu na fadada karfin ikonsu.

Daga karshe ma’aikatar ta nuna cewa duk wani zargi da ake yi wa yan kasar baharain da ake danganta shi da kasar iran ba shi da tushe balle madafa

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted