dakarun kare juyin musulunci na kasar iran sun ce sun kai hari da jirgi mara matuki kan naurar rada ta tsaro a sansanin sojojin amurka na shaikh isa dake kasar baharain, kuma ta bayyana farmakin a matsayin mayar da martani game da ci gaba da keta sararin samaniyar kasar iran da jirage marasa matuki da Amurka ke yi
haka zalika dakarun na IRGC sun jaddada cewa ci gaba da keta hurumin sararin samaniyar iran da amurka ke yi da yin amfani da makamanta dake sansanoninta a yankin ba zai tafi hakan nan ba, ba tare da mayar da martani ba, kwamandan sojojin amurka ne ke da alhakin duk abin da ya biyo baya sakamakon abin da take aikatawa
wanann bayani ya zo ne bayan sanarwa da dakarun IRGC suka fitar a ranar jumaa cewa jiragen saman yaki na kasar iran sun tarwatsa naurar radar amurka a sansaninta dake kasar baharain a matsayin gargadi da jan kunne
Daga karshe IRGC ta bayyana wannan mataki a matsayin gargadi mai tsananin ga makiya masu cin zarafi don su dakatar da tsokana ta sama da kuma fasa kwabrin man fetur a mashigar hormuz