Ministocin harkokin waje na kasashen da ke cikin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta (ECO) sun yi kira da a kawo karshen yakin da Amurka ke yi da Iran, suna nuna goyon bayansu ga sabon shirin da Tehran ta yi na kawo karshen yakin da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.
Ministocin sun bayyana hakan ne a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a karshen taron Majalisar Ministocin karo na 30 a birnin Islamabad, na kasar Pakistan.
Sun bayyana damuwa game da yanayin tsaro a yankin bayan harin da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran, kuma sun amince da shawarar Iran na kawo karshen yakin har abada.
Sanarwar ta kuma jaddada mahimmancin nuna goyon baya ga kokarin shiga tsakani da Pakistan da Qatar ke yi don rage tashin hankali a yankin.
Kasashen membobin ECO sun kara jaddada muhimmiyar rawar da Iran ke takawa wajen ciyar da manufofin kungiyar gaba, suna bayyana Jamhuriyar Musulunci a matsayin daya daga cikin membobin da suka kafa ta.
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da Iran ta gabatar da “shiri na kwanaki biyu” wanda zai iya share fagen sake bude mashigin tekun Hormuz da kuma ci gaba da tattaunawa.
Tehran ta bayyana a fili cewa dole ne Washington ta cika sharudda bakwai kafin Iran ta amince ta ci gaba da tattaunawar diflomasiyya.