Iran Ta Yi Tir Da Fuska Biyun Da Wasu Kasashe Suke Nunawa

Jakadan jumhuriyar Musulunci ta Iran (JMI) a MDD ya tit da wasu kasashe masu nuna fuska biyu idan ana maganar makamashin Nukliya a duniya. Tashar

Jakadan jumhuriyar Musulunci ta Iran (JMI) a MDD ya tit da wasu kasashe masu nuna fuska biyu idan ana maganar makamashin Nukliya a duniya.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Gholamhossein Darzi, yana fadar haka a jiya Litinin ya kuma kara da cewa, wasu daga cikin kasashen saboda rashin adalci da kiyayya ga JMI sun kasa ko yin allawadai da hare haren da aka kaiwa cibiyoyin Nukliya na JMI. A cikin wannan halin ne suke kiran JMI ta hada kai da hukumar makamashin Nukliya ta Duniya IAEA.

Darzi ya bayyana haka ne a jawabinda da ya gabatar a cibiyar MDD a kuma taron samar da yanking abas ta tsakiya wacce bata da makaman Nukliya ko makaman kare dangi.   Y ace, fuska biyu wanda wadan nan kasashe suke nunawa wani zagon kasa ne ga shirin kwance damarar makaman Nukliya a yankin gabas ta tsakiya. Ya ce wannan yana faruwa ne a dai dai lokacinda duk duniya tana ganin yanda HKI take kara kissan al-ummar Gaza, da yunwa da rashin bada damar a shigo da kayakin agaji don samar da rayuwa maid an mutunci ga Falasdinawa.   Amurka da Haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) sun kai hare hare har sau biyu a cikin shekaru 2025 da 2026 amma hatta hukumar IAEA da kanta ta kasa yan allawadai da wadannan kasashe masu makaman nukliya da kuma kare dangi yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted