Iran Ta Musanta Zargin Kashe Shuwagabannin Yamma

Kakakin ma’aikatar harkokin wajne kasar Iran Esmael Bakhaie, ya yi watsi da zargin cewa gwamnatin jumhuriyar Musulunci ta Iran (JMI) tana shirin kashe wasu Jami’an

Kakakin ma’aikatar harkokin wajne kasar Iran Esmael Bakhaie, ya yi watsi da zargin cewa gwamnatin jumhuriyar Musulunci ta Iran (JMI) tana shirin kashe wasu Jami’an gwamnatin kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran yanakalto Baghaei yana fadar haka a jiya litinin, ya kuma kara da cewa, haramtacciyar kasar Isra’ila ce take kirkiro ta kuma yada labaran karya kan cewa Iran tana shirin kashe wasu jami’an gwamnatocin kasashen yamma don sanya rudani da kuma fargaba a cikin wadan nan kasa she, don kuma a sake komawa tashin hankali ko yaki kan kasar Iran.

Labarin ya bayyana cewa Baghaei ya bayyana haka ne a shafinsa na X , tana yin haka ne don samarwa masu son yaki cikin Jami’an gwamnatocin Amurka da kasashen turai goyon bayan mutanen kasar, don su sake farwa kasar Iran da yaki.

Kafin haka Isra’ila da Amurka sun kashe Jami’an gwamnati da kuma masana fasahar Nukliya na kasar Iran daga cikin har da Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Imam Sayyid Aliyul Khaminaei (q) da iyalan gidansa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted