rahotanni sun nuna cewa kungiyar hizbullah ta kasar labanon ta yi tir da harin da sojojin HKI suka kai kan motar sojin kasar labanon a kudancin berut da ya kai ga shahadar sojoji 3 ciki har da manyan jami’ai guda biyu.
haka zalika ta bayyana cewa wannan harin sakamako ne na yadda gwamnati take nuna rashin kulawa da hakki da rayukan alummar kasar yadda ta mika wuya kyauta ga abokan gaba a kwanan nan, a Washington, hakan ya kara karfafa gwamnatin sahyuniya ci gaba da zub da jiin mutanenmu da sojojin mu.
hizbullah ta mika ta’aziya ga iyalan wadanda a abin ya shafa da kuma rundunar sojojin kasar da kwamandoji da manya da kananan sojojin kasar, game da wannan babban rashi da aka yi sakamakon harin zalunci na isra’ila.
Wani labari da kafafen yada labaran kasar labanon suka fitar ya nuna cewa mutane 6 ne suka mutu wasu guda 4 kuma suka jikkata sakamakon harin da sojojin isra’ila suka kai ,a garin saksakiya dake yankin sidon a kudancin kasar labanon.