Hamas Tayi Watsi Da Shirin Amurka Na Kafa Sabon Kawance A Yankin

kungiyar gwagwarmayar musulunci ta hamas  tayi tir da bayanan baya bayan nan  da fira ministan isra’ila yayi game da batun kafa sabuwar kawance da za

kungiyar gwagwarmayar musulunci ta hamas  tayi tir da bayanan baya bayan nan  da fira ministan isra’ila yayi game da batun kafa sabuwar kawance da za ta kunshi kasashen larabawa wanda wannan nuna rashin damuwa ne da kasashen larabawa a fili, kuma barazana ce kai tsaye ga manufofinsu

kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem yace Natanyaho yana kokarin sake fasalin yankin ta yadda zai koma yana kare manufofin gwamantin mamaya.

wannan tsokacin ya zo ne bayan da Binjamin na tanyaho yayi ikirarin cewa isra’ila tana shirin sake kafa wani kawance da wasu kasashe da suka hada da kasashen indiya, Girka, Cyprus, da kuma wasu kasashen larabawa da kasashen Afrika da na Asiya

haka zalika Qaseem ya bayyana cewa gwamnatin sahyuniya ta bukaci kafa sabon kawance da goyon bayan Amurka  domin kara kiyaye manufofinta da ciyar da su gaba  da suka yi hannun riga da na kasashen larabawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted