Hamas Ta Yi Wa Isra’ila Ruwan Rokoki Tun Daga Rafah

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce ta kaddamar da sabbin hare-hare na rokoko kan Isra’ila a ranar Lahadi, a daidai lokacin da sojojin gwamnatin

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce ta kaddamar da sabbin hare-hare na rokoko kan Isra’ila a ranar Lahadi, a daidai lokacin da sojojin gwamnatin kasar ke kai hare-hare a kudancin birnin Rafah.

Hamas ta ce ta harba rokoki akalla takwas kan Tel Aviv da kewaye, yayin da aka harba wasu makaman roka a wasu garuruwa dake karkashin mamayar Isra’ilar.

Wannan shi ne karo na farko cikin kusan wata hudu da kungiyar Hamas ta harba makamin roka zuwa yankin Tel Aviv da ke tsakiyar Isra’ila.

Sojojin Isra’ila sun ce akalla makaman roka takwas aka harba zuwa yankin Tel Aviv daga Rafah a kudancin Gaza, suna masu cewa sun samu nasarar kakkabo wasu daga ciki, sai dai babu rahoton jikkata.

A ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata ne Isra’ila ta kaddamar da kazamin yakinta kan Gaza bayan da kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu ta kai wani farmaki kan Isra’ila a matsayin ramuwar gayya kan irin ta’asar da take ci gaba da yi wa al’ummar Palasdinu.

Tun bayan fara kai hare-hare a zirin Gaza, Isra’ila ta kashe Falasdinawa kusan 36,000 galibi mata da kananan yara, yayin da wasu 80,643 suka jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments