rahotanni sun bayyana cewa kungiyar Hamas ta yi tir da barazanar da Isra’ila ke yi na share yan gwagwarmaya baki daya, yace ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta a yankin Gaza, yana nuna irin yadda tayi biris da yajejeniyar kasa da kasa da kuma kokarin diflomasiya na dakatar da kisan kare dangi da take yi.
a cikin wani bayani da kakakin kungiyar hamas Hazem Qasem ya fitar ya soki tsokacin da ministan kudi na Isra’ila bazalel smotrich yayi inda yace zabin da ya ragewa Isra’ila shi ne share kungiyar hamas, kuma sun yanke shawarar bawa shugaban Amurka Donald trumph damar ya shiga lamarin ta irin hanyarsa .
kakakin ya kara cewa ci gaba da dauka mataken soji da Isra’ila ke yi da barazana yana nuna irin yadda take yin zagon kasa da gangan kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta da kuma matsin lamba kan alummar falasdinu.
daga karshe yayi kira ga hukumomi na kasa da kasa su sanya tankunkumi kan isara’ila ,kuma yayi maraba da bayanan da wasu kasashen 20 suka fitar na yin Tir da Isra’ila game da mataken da take dauka na karbe ikon kula da gabar yammacin kogin jodan , yace wannan matakin zai kara jefa yankin cikin rashin tsaro da zalunci.