Hamas Ta Soki Isara’ila Kan Hana  Falasdinawa Zuwa Masallacin Kudus A Lokacin Watan Ramadan

kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta ce isra’ila tana takurawa falasdinawa sosai wajen isa zuwa ga masallacin kudus a ranar farko na watan Ramadan domin karya

kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta ce isra’ila tana takurawa falasdinawa sosai wajen isa zuwa ga masallacin kudus a ranar farko na watan Ramadan domin karya karfin zuciyar alummar falsdinu.

kungiyar tayi kira ga alummar falasdinu da su ci gaba da yin tururuwa zuwa masallacin kudus, don amfana da albarkatun dake cikin watan Ramadan mai alfarma, kuma su kare masallacin daga makircin da yan mamaya ke kullawa kansa

kungiyar ta ce da gangan sojojin Isra’ila suka cin zarafin masu ibada da suke kokarin isa zuwa masallacin kudus ta hanyar daukar  tsauraran mataken soji da sojojin  ke dauka,

daruruwan falasdinawa ne aka hanasu isa zuwa masallacin kudus don gudanar da ibada tun daga kan shingaye da suka sanya, dama tun da farko gwamnatin isra’ila tace za ta ba da dama ga falasdinawa 10,000 ne kwai su shiga masallacin kudus domin yin sallamar juma’a, kuma maza wadanda shekarunsu ya haura 55, mata kuma yan shekaru 50, da kuma yara yan shakara 12 dake tare da wani babba daga cikin iyalinsa

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted