Hamas Ta Fitar Da Sakon Juyayin Shahadar Shugabanta Isma’il Haniya

Kungiyar Hamas ta fitar da wata sanarwa tana mai cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas tana taya al’ummar Palastinu da al’ummar Larabawa da Musulmi da

Kungiyar Hamas ta fitar da wata sanarwa tana mai cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas tana taya al’ummar Palastinu da al’ummar Larabawa da Musulmi da kuma dukkanin ‘yantattun al’ummar duniya, juyayin shahadar shugaba dan uwa, Mujahidi,  Ismail Haniyeh.

Sakon na Hamas na a matsayin sanarwa a hukumance daga bangaren kungiyar kan shahadar Isma’il Haniya, yayin da sauran kungiyoyi da bangarori daban-daban na Falasdinawa suke ci gaba da fitar da sakonni daban-daban a cikin yanayi an fushi dab akin ciki kan wanann mummunan aikin ta’addanci na Isra’ila.

Tun kafin wannan lokacin dai Isra’ila ta jima tana neman hanyar da za ta aiwatar da kisan gila a kan Isma’il Haniya, wanda ya sha tsallake rijiya da baya a hare-haren Isra’ila tun lokacin da yake rayuwa a Gaza .

Isma’il Haniya yana daga cikin mambobin kungiyar Hamas na farko tun lokacin kafa kungiyar, wanda kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen karfafa kungiyar da kuma jagorantar ayyukanta a ciki da wajen Falastinu.

Haniya ya karbi jagorancin kungiyar Hamas ne daga hannun tsohon shugaban kungiyar Khalid Mash’al, Haniya shi ne shugaba na hudu na kungiyar Hamas tun daga lokacin da aka kafa ta. Babu wani bayani ya zuwa yanzu a hukumance kan wanda zai jagoranci kungiyar bayan shahadar Isma’il Haniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments