Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta sanar da kashewa, da raunatawa, da kuma kame wasu sojojin Isra’ila, ta hanyar kai musu hari a arewacin zirin Gaza.
Abu Obeida, kakakin kungiyar al-Qassam Brigades, reshen soji na Hamas ne ya bayar da wannan bayanin a wani faifan faifan bidiyo yau Lahadi.
Lamarin ya faru ne a yayin wani harin kautan bauna a hanyoyin karkashin kasa a sansanin ‘yan gudun hijirar na birnin Jabalia, in ji shi.
Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba.
Kusan Falasdinawa 36,000 galibi mata da kananan yara ne suka mutu sakamakon mummunan farmakin da sojoji suka fara tun bayan harin ba zata, da kungiyar Hamas ta kai.