Hamas: Kutsawar ‘Yan Share Wuri Zauna A cikin Masallacin Kudus Kokarin Tayar Da Yakin Addini Ne

Wani jami’in kungiyar Hamas Harun Nasiruddin  ya bayyana cewa, kutsawar da yahudawa ‘yan share wuri zauna suke yi a cikin masallacin Kudus yakin addini ne,

Wani jami’in kungiyar Hamas Harun Nasiruddin  ya bayyana cewa, kutsawar da yahudawa ‘yan share wuri zauna suke yi a cikin masallacin Kudus yakin addini ne, kuma yana a karkashin kokarin da mayar da masallacin na yahudawa.

Nasiruddin ya kuma ce; Abinda yake faruwa yana nuni ne da  tsattsauran ra’ayin ‘yan sahayoniya  wanda kuma yake samun cikakken goyon bayan hukumar “Isra’ila”.

‘Yan share wuri zauna suna shiga cikin harabar masallacin Kudus daga lokaci zuwa lokaci, tare da yin ibadunsa na yahudanci.

Shi dai masallacin Kudus yana a matsayin na uku bayan masallacin Ka’aba da masalalcin Annabi ( a.s) a Madina.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted