Hamas: Isra’ila Ta Lalata Duk Wani Abu Mai Amfani A Yankin Gaza

isra'ila ta kassara yankin gaza inda inda ta lalata komai na rayuwar alumma,

Rahotanni daga yankin gaza sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta ce Gwamnatin sahyuniya ta lalata duk wami abu mai amfani a rayuwa  a yankin Gaza da gangan, inda ta rusa dukkan abubuwan more rayuwar alumma da muhimman wurare, bayan haka kuma ta tarwatsa cibiyar dake samar da ruwan sha, domin jefa alumma cikin kishi

A cikin bayanin da ya fitar a jiya litinin kakakin kungiyar Hamas Hazem Qaseem yayi tir da harin da Isra’ila ta kai a cibiyar samar da ruwan sha na Al-ridwan dake yankin Gaza, a ci gaba da yakin kare dangi da take yi kan alummar falasdinu, kuma ta kai harin ne da jirgin yaki , haka kuma ta kai wani harin kan wani masallaci dake kusa da wurin inda ta tarwatsa shi da gidajen da ke wurin .

kungiyar Hamas ta bayyana cewa irin wadannan hare hare na rashin tausayi da isra’ila ke kawai ya kai kololuwarsa , bayan ta yi watsi da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma wanda aka sanyawa hannun tsakaninta da Hamas da shugaban Amurka Donald Trump ya jagoranta da shiga tsakanin kasashen Masar turkiya da kuma Qatar

Ma’aikatar lafiya ta yankin Gaza ta sanar cewa daga lokacin da Isra’ila ta kaddamar da yakin kare dangi a gaza a ranar 7 ga watan oktoba shekara ta 2023 kimanin falasdinawa 73422 ne suka yi shahada yayin da 174401 kuma suka jikkata sama da falasdinawa 1286 kuma an kashe su ne bayan sanar da abin da aka kira tsagaita wuta, da ya fara aiki a watan oktoban shekara ta 2025

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted