Search
Close this search box.

Hamas: farmakin Isra’ila kan Rafah ba zai ba ta nasara kan Falastinawa ba

Shugaban kungiyar Hamas, Osama Hamdan, ya gudanar da wani taron manema labarai, inda ya tabbatar da cewa, farmakin da sojojin Isra’ila suka kai a Rafah,

Shugaban kungiyar Hamas, Osama Hamdan, ya gudanar da wani taron manema labarai, inda ya tabbatar da cewa, farmakin da sojojin Isra’ila suka kai a Rafah, bas u fita lafiya ba kamar yadda suke tunani.

Ya mai jaddada cewa kungiyar ta nuna sassauci matuka, da ingantacciyar hanya domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Shugaban kungiyar Hamas, Osama Hamdan, ya tabbatar a ranar Talata cewa, farmakin da sojojin Isra’ila suka kai a Rafah, “ba zai zama yawon shakatawa a gare su ba, kamar yadda kuma haka yake a dukkan yankunan Falastinawa da suka kutsa kai.

A yayin taron manema labarai da ya gudanar a birnin Beirut na kasar Labanon, Hamdan ya yi magana game da amincewar da kungiyar ta Hamas ta yi  da kudirin da masu shiga tsakani a Masar da Qatar suka gabatar, yana mai bayanin cewa hakan ya zo ne “sakamakon doguwar tattaunawa mai wahala da sarkakiya na tsawon makonni da ma watanni da suka gabata.

Hamdan ya yi nuni da cewa, Hamas ta “tsaya kan bukatunta, amma duk da hakan ta nuna sassauci a inda ya dace.

Hamdan ya jaddada cewa, wannan amincewar ta zo ne bisa la’akari da nauyin da kungiyar ke da shi a gaban al’ummar Palastinu a zirin Gaza, da kuma tsananin damuwar da suke da ita kan muradunsu, hakkokinsu, da sadaukarwarsu, da kuma nuna dattako ga rawar da masu shiga tsakani suka taka wajen cimma wannan yarjejeniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments