Gwamnatin Nijar Ta Zargi Faransa Da Wasu Kasashen Yammacin Afirka Da Shirya Kai Harin Birnin Yamai

Shugaban gwamnatin sojan kasar Nijar ya zargi kasashen Faransa, Benin da Cote De Voire da shirya harin da aka kai wa filin saukar jiragen sama

Shugaban gwamnatin sojan kasar Nijar ya zargi kasashen Faransa, Benin da Cote De Voire da shirya harin da aka kai wa filin saukar jiragen sama na birnin Yamai a daren Alhamis.

Janar Abdurrahman Tchiani ya fada wa tashar talabijin din kasar cewa; “Muna tunatar da wadanda su ka dauki nauyin wannan ‘yan dabar, da su ne Emmanuel Macron ( shugaban kasar Faransa), Patrice Talon             ( shugaban kasar Benin) da Alassane Outara ( shugaban kasar Cote De Voire) da cewa, mun ji haushin da su ka yi, abinda ya saura shi ne su saurari Gurnani irin na zaki daga gare mu.”

A daren Alhamis ne dai mazauna birnin Yamai su ka rika jin harbe-harbe da aka rika yi a kusa da filin saukar jiragen sama na tsawon sa’o’i..

Wani shaidai ganin ido ya fada wa manema labaru cewa an ji karar fashewar abubuwa masu karfi a tsakar daren Alhamis a kusa da filin saukar jiragen saman a Diori Hamani, kafin daga baya karar da rika raguwa sannu a hankali.

Wani matashi mai suna Ibrahim Bubakar  wanda yake rayuwa a kusa da filin saukar jiragen saman  ya fadi cewa;

 “Mun tsorata. Kuma da yara a kusa da ni, duk muna rike da carbi muna ta rokon Allah ya kare mu, muna kuma rokon dukkanin ‘yan kasa akan su yi ta yi wa kasarmu Nijar addu’a.”

Sai dai a wata sanarwa da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar ta bayyana cewa; Maharan ‘yan ta’adda ne, kuma an kashe 20 daga cikinsu, yayin da su kuma su ka kashe sojojin kasar biyu. Bugu da kari, jami’an tsaron na Nijar sun yi nasarar kama wasu ‘yan ta’addar su 11.

Tuni dai kungiyar ISIS mai ikirarin jihadi ta sadar da daukar nauyin kai nari akan wani sansanin sojan sama dake a filin saukar jiragen sama na Diori Hamani.

Kungiyar ta fitar da wannan sanarwar ne dai a wani sako da ta wallafa kafar watsa labarunta ta “A’amaq” tare da bayyana shi da cewa; hari ne na ba za ta, wanda kuma an tsara shi da kyau.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted