Gwamnatin Kenya Ta Ci Gaba Da Tono Gawarwakin Da Masu Tsaurin Addinin Kirista Da Suka Kashe Kansu A Kenya

Kenya ta tono gawarwakin mutane 32 a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna bacin ransu kan mace-macen ‘yan darikar addini masu tsattsauran ra’ayi

Kenya ta tono gawarwakin mutane 32 a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna bacin ransu kan mace-macen ‘yan darikar addini masu tsattsauran ra’ayi

Hukumomin kasar Kenya sun tono gawarwaki 32 a makon da ya gabata a kudu maso gabashin kasar, wani sabon bala’i da ya sake haifar da sukar gwamnatin kasar, wadda a baya ta yi alkawarin murkushe kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi bayan mutuwar daruruwan mabiya kungiyar asiri ta “Apocalypse” shekaru biyu da suka gabata.

Gwamnatin Kenya da mazauna yankin sun danganta gawarwakin da aka gano a kauyen Kwa Binzaro da wata kungiyar kiristoci da ake zargi da hannu wajen kashe mutane fiye da 400 a dajin Chakahola da ke kusa a shekarar 2023.

Babban likitan gwamnati a yankin Richard Njoroge, ya ce an sake gano karin gawarwakin mutane bakwai a ranar Alhamis din da ta gabata, wanda ya kawo adadin suka kara yawa tun da aka fara tonon gawarwakin makon jiya zuwa 32.

An ci gaba da binciken a ranar Juma’a, tare da ma’aikatan sanye da fararen kaya masu kariya da safar hannu shudi suna ta kutsawa cikin daji tare da shebur da kuma sauran kayan aiki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted