Gwamnatin Kasar Afrika Ta Kudu Ta Fara Shirin Hukunta Masu Nuna Kin Jinin Baki A kasar

Gwamnatin Afrika ta Kudu ta sha alashin daukar mataki mai tsauri kan masu nuna wariya da kuma kin jinin baki a fadin kasar, wanda ya

Gwamnatin Afrika ta Kudu ta sha alashin daukar mataki mai tsauri kan masu nuna wariya da kuma kin jinin baki a fadin kasar, wanda ya zuwa yanzu an kwashe tsawon makonni ana rigimar korar baki a Afrika ta Kudu matakin da ya kai ga hallaka wasu bakin.

Da yake jawabi a kafar Talabijin din kasar shugaba Cyril Ramaphosa, ya musanta zargin masu korar bakin hauren cewa baki sune ke haddasa matsalolin da ke faruwa a kasar.

A cewar shugaban, an farfado da hukumar da ke dakile  rikicin da ya shafi nuna kin jinin baki wadda aka kafata tun 2014, lokacin da kasar ta shedi irin wannan rikici da ya haddasa mutuwar mutane da dama,.

Ko da yake Ramaphosa ya ce kasar a cikin shekaru 2 da suka gabata ta mayar da bakin haure 100,000 zuwa kasashensu bayan tabbatar da cewa sun shiga kasar ne ba bisa ka’ida ba, amma ya amince cewa dokokin kwararar bakin haure na kasar suna da rauni kuma za’a duba da kuma sake nazartarsu.

Afrika ta Kudu ta yi kaurin suna a kin jinin bakin haure, kuma bakaken fata, kuma an ga yadda wannan rikici yayi ajalin mutane sama da 60 a 2008.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted