Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kore hannunta a hatsarin jirgin saman shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi
Rahotonni sun bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi gaggawar kore hannunta a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu na shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi da mukarrabansa, tun kafin Iran ta sanar da tabbacin mutuwarsu a hukumance.
Masharhanta sun bayyana matakin na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da cewa: Nuna damuwa ce game da sakamakon abin da ya faru a fagen fama a yankin Gabas ta Tsakiya, da kuma yiwuwar Iran ta yi amfani da shi wajen kara kai hare-hare kan haramtacciyar kasar ta Isra’ila. A nasu bangaren, Kwararru a haramtaccioyar kasar Isra’ila sun nisanta yiwuwar bullar duk wani tashin hankali a tsakanin bangarorin biyu sakamakon hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu, kuma sua tsammani duk abin da zai faru zai biyo bayan sakamakon da Iran ta kai gare shi ne kan binciken da zata gudanar kan lamarin da ya kai ga shahadar Shugaban kasar.