Ministan harkokin wajen kasar Ghana Samuel Okudzeto Ablakwa ya sanar da cewa, ‘yan kasar 55 ne aka kashe a yakin da ake yi a tsakanin kasashen Rasha da Ukiraniya.
Ministan harkokin wajen kasar ta Ghana ya bayyana haka ne daga birnin Kieve na kasar Ukiraniya inda ya je domin karbar wasu ‘yan kasar biyu da aka kama a matsayin fursunonin yaki suna taya Rasha yaki.
Haka nan kuma ya ce, ya sami bayanai akan cewa da akwai ‘yan kasar 272 da aka shigar da su cikin yakin kasashen na Rasha da Ukiraniya wanda ya barke tun a 2022, yana mai cewa, an yi wasa da hankalinsu ne da kuma yaudararsu da wasu kungiyoyin masu aikata laifi su ka yi.
Ablakwa ya kuma ce; gwamnatin kasarsa tana aiki tukuru domin rusa kungiyoyin da suke yaudarar mutane suna shigar da su cikin wannan rikici.
A cikin watannin bayan nan dai da akwai ‘yan kasashen Afirka da daka da su ka shiga cikin yakin kasashen Ukiraniya da Rasha, mafi yawancinsu suna bangaren Rasha.
Gwamantocin kasashen Afirka suna bayyana cewa, ana daudadar ‘yan nahiyar ne da sunan sama musu wasu ayyuka masu tsoka.
Ministan harkokin wajen kasar Ukiraniya ya fada a ranar Larabar da ta gabata cewa, da akwai ‘yan Afirka kusan 1,800 daga kasashe 36 da suke yaki a cikin sojojin Rasha.
‘yan kasar Ghana ne su ka fi mutuwa a yakin, a tsakanin sauran ‘yan kasashen nahiyar ta Afirka da aka sanar zuwa yanzu.
A can kasar Kamaru, wata kafar watsa labaru ta sanar da cewa; da akwai ‘yan kasar 94 da su ka mutu a wajen yaki, sai dai babu tabbaci daga mahukuntan kasar.
Ita ma kasar Afirka ta kudu ta ce, da akwai ‘yan kasar biyu, sai kuma wani dan kasar Kenya daya da suk an kashe su wajen yi wa Rasha yaki.
Rasha ta sha kore cea tana daukar ‘yan Afirka domin su yi mata yaki da Ukiraniya.