Falasdinawa kimani 120 suka kai ga shahada ya zuwa yanzu tun bayan da sojojin HKI suka fara kai hare hare a kan garin. Majiyar kamfanin dillancin lanaran IRIB-NEWS a nan Tehran ya nakalto kwamitin ayyukan bada agajin gaggawa na garin Rafah yana cewa a tsakanin ranakun Asabar da Lahadi da suka gabata kadai sojojin yahudawan sun kai falasdinawa 30 ga shahada.
Kwamitin ya kara da cewa tun bayan soma hare hare na bayan nan a garin Rafah sojojin HKI sun tilastawa dubban Falasdinawa ficewa daga garin zuwa tsakiya da wasu waurare a cikin yankin na Gaza.
Labarin ya kara da cewa rufe kofar shiga ta Rafa wanda sojojin HKI suka yi a ranar litinin da ta gabata, ya kara tsananta rayuwar falasdinawa kimani miliyon 1.3 da suke rayuwa a garin. Mafi yawan mutane a Rafah yan gudun hijira ne daga sauran yankunan Gazi.
A makon da ya gabata ne majalisar ministocin HKI ta yanke shawarar kaiwa Falasdinawa hare hare a Rafah duk tare da gargadin kasashen duniya kan kada ta yi hakan saboda za’a rasa rayuwan falasdinawa masu yawa.
Fiye da watanni 7 ke nan da fara yaki a gaza sojojin HKI sun kashe Falasdinawa fiye da dubu 35 a yayinda wasu kimani dubu 79 suka ji rauni.