Majiyar kafafen yada labarai a Gaza sun bada labarin kashe wani Jami’in tsaro na kungiyar Hamas wanda yake kula da rabon kayakin agaji a yankin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto majiyoyin labarai a gaza na cewa hukumar Leken Asira ta Shabak ta HKI sun kai kai Burgeniya Janar Fayeq Al-Mabhouh ga shahadi ne a lokacinda suka kai hare hare kan asbitin Asshifa a zirin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran SAMA na gwamnatin Falasdinawa a Gaza ya bayyana cewa Al-Mabhouh ya kasance jami’in dansanda a Gaza, kuma yana aiki da hukumomin agaji na UNRWA da kuma kabilun yankin saboda isar da kayakin agaji ga mabukata.
Amma majiyar yahudawan sahyoniyya sun bayyana cewa sun yi musayar wauta da Al-Mabhouh a asbitin shifa kafin su kashe shi.
Sojojin HKI sun dau kwanaki suna mai hare haren kan asbitin asshifa na Gaza, tare da jiragen yaki da kuma makaman tankunan yaki.
Banda haka labarin ya kara da cewa Al-Mabhour shi ne babban jami’in yansanda na Gaza mai kula da tsarin cikin gida a a Gaza.