Shugaban kungiyar ‘Jahadul Islami’ daya daga cikin manya manyan kungiyoyi masu gwagwarmaya da yahudawa Sahyoniyya a Gaza, ya gana da babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci a Iran shawara kan harkokin kasa da kasa Ali Wilayati
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya kara da cewa Ali Wilayati ya gana da Nakhalah da tawagarsa a ofishinsa da ke nan birnin Tehran. Inda banga rorin biyu suka tattauna halin da ake ciki a Gaza da kuma Falasdinu da aka mamaye.
Wilayati ya bayyana cewa jarunta da hakuri da kuma turjiyar da mutanen Gaza sukan nuna a cikin watanni kimani 6 da suka gabata ya zama abin alfahari da kuma jinjina. Ya kumakara da cewa kungiyoyin Falasdinawa masu gwagwarmaya a Gaza, sun wargaza dukkan shirye shiryen HKI da magoya bayanta a duniya, dangane da kasar Falasdinu da kuma yankin Asia ta kudu.
Kuma da yardarm All…kasar Falasdinu da aka mamaye zata kubuta daga hannun HKI da kuma kasashen yamma, kuma falasdinawa wadanda suka bada dubban shahidai a wannan yakin zasu rayu a kasarsu ba tare da wadan nan azzaluman kasashen sun yi katsalanda a cikin al-amarin kasarsu ba.
Ya kuma kammala da cewa HKI ba zata kai ga manufofinta a wannan yakin ba, duk tare da tallafin da take samu daga kasashen yamma musamman Amurka.