Iran: Jakadiyar Kasar Bolivia Ta Taya Iran Juyayin Wadanda Hare Hare Kan Ofishin Jakadancinta A Siriya Suka Kai Ga Shahada

Jakadiyar kasar Bolivia a nan Tehran ta yiwa JMI jajen hare haren ta’addancin da HKI ta kai kan karamin ofishin jakadancin kasar a birnin Damascus na kasar Siriya. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Romino Parasromus jakadiyar kasar Bolivia a Tehran tana fadar haka a jiya Laraba Ta kuma kara da cewa, […]
Gaza: Nakhala, Ya Gana Da Wilayati Dangane Da Yakin Tufanul Aksa A Tehran

Shugaban kungiyar ‘Jahadul Islami’ daya daga cikin manya manyan kungiyoyi masu gwagwarmaya da yahudawa Sahyoniyya a Gaza, ya gana da babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci a Iran shawara kan harkokin kasa da kasa Ali Wilayati Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya kara da cewa Ali Wilayati ya gana da Nakhalah […]
Iran: Jagora Ya Bukaci A Kawo Tunanin Mutane Da Dukiyoyinsu Cikin Manufar Tabbatar ‘Shi’arin’ Wannan Shekarar

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khamina’e ya bukaci gwamnatin shugabab Ra’isi ta sanmar da wani kwamiti wanda zai yi aiki a cikin kasa, don jawo hankalin mutane su zuba dukiyoyinsu don bunkasa tattalin arzikin kasar. Kamfanin dillancin labaran IRNA ya nakalto Jagoran yana fadar haka a lokacinda yake […]
Iran: Jami’an Tsaro Na Kan Iyaka Wadanda Aka Kaiwa Hari A Sistan Buluchistam Sun Yi Shahada

Iran: Jami’an Tsaro Na Kan Iyaka Wadanda Aka Kaiwa Hari A Sistan Buluchistam Sun Yi Shahada
Ana Cigaba Da Yin Allawadai Da Harin HKI Akan Karamin Ofishin Jakadancin Iran A Syria
Kasashen Tajikistan da Kazhaskistan sun shiga cikin jerin masu yin tir da harin sojojin HKI akan karamin ofishin jakadancin Iran a Syria. A wani bayani da ma’aitakar harkokin wajen Tajikistan ta fitar ta yi Allawadai da harin na HKI akan karamin ofishin jakadancin Iran ,tare da bayyana shi a matsayin wanda yake cin karo da […]
HKI Na Cigaba Da Kai Wa Kudancin Lebanon Hare-hare

Sojojin HKI suna cigaba da kai wa kauyuka da garuruwan dake kudancin Lebanon hare-hare ta hanyar amfani da nau’oin makamai. Daga cikin garuruwan da sojojin HKI su ka kai wa hari a jiya Laraba da a kwai “Ramiyah”, Aynat da Balida. A gefe daya kungiyar ta Hizbullah ta kai wa sansanoni da cibiyoyin ‘yan mamaya […]
Gaza: Adadin Falasdinawan Da Su Ka Yi Shahada Ya Haura 32,000

Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta ce Adadin wadanda su ka yi shahadi sun kai 32, da 975, wadanda suka jikkata kuma sun kai 75,000 da 577. Kaso 70 % na wadanda su ka yi shahadar da kuma jikkata mata ne da kananan yara. Har ila yau wannan sanarwar ta ce; A halin yanzu da […]
HKI Tana Cigaba Da Hana Shigar Da Kayan Agaji Zuwa Zirin Gaza

Kamfanin dillancin labarun “Irna” na Iran ya nakalto hukumar agaji ta “UNRWA” tana cewa, HKI tana cigaba da hana a shigar da kayan agaji zuwa zirin Gaza Sanarwar ta kuma ce, HKI ta hanawa ma’aikatan hukumar ta “UNRWA” kai wa mazauna Arewacin Gaza, kayan agaji. Phillip Lazariani wana shi ne babban jami’in hukumar Agajin ta […]