Gaza: Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) Ta Bada Sanarwan Cewa Sojojin HKI Sun Kai Hare Hare Fiye Da 400 Kan Asbitoci A Gaza

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bada sanarwan cewa sojojin HKI sun kai hare hare kan asbitoci da cibiyoyin kiwon lafiya fiye da 400 a Gaza

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bada sanarwan cewa sojojin HKI sun kai hare hare kan asbitoci da cibiyoyin kiwon lafiya fiye da 400 a Gaza tun bayan fara yakin Tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban da ya gabata.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Margaret Harris mai magana da yawun hukumar tana fadar haka a jiya Laraba a shafinta na X daga birnin Geneva.

Margaret Harris  ta kara da cewa sojojin HKI sun kashe likitoci da ma’aikatan kiwon lafiya har 685 a wadannan cibiyon kiwon lafiya, sannan wasu 902 suka ji rauni. Hare haren har iyalai sun lalata kayakin kiwon lafiya akalla 99.

Margaret Harris  ta kara da cewa sojojin HKI sun kai kashi 38% daga cikin wadanan hare hare a birnin Gaza, sai kashi 23% a arewacin birnin Gaza sannan kashi 28% a kudancin Gaza wadanda suka hada da garin Khan Yunus da wasu wurare a yankin.

Daga karshe Jami’ar ta WHO ta bayyana cewa kofar ragon da HKI tayiwa Gaza ya tabbatar da cewa tana aikata laifin yaki don sanadiyyar haka falasdinawa musamman jarirai suna mutuwa saboda karancin abinci da kuma yunwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments