Gaza : Afirka Ta Kudu, Ta Sake Garzayawa Kotun ICJ, Kan Farmakin Isra’ila A Rafah

Kasar Afrika ta Kudu, ta sake komawa Kotun Duniya ta (ICJ), inda take neman kotun ta fitar da wani sabon umarni kan Isra’ila, wadda ta

Kasar Afrika ta Kudu, ta sake komawa Kotun Duniya ta (ICJ), inda take neman kotun ta fitar da wani sabon umarni kan Isra’ila, wadda ta zargi a watan Disamba da laifukan kisan kiyashi.

A wannan karon, Afirka ta Kudu ta nuna damuwa da halin da ake ciki a Rafah, inda sojojin Isra’ila ke dannawa.

Pretoria ta bukaci alkalai da su umurci Isra’ila ta janye daga birnin.

Ta hanyar karbe iko da kan iyaka da Masar, da mashigar Kerem Shalom, Isra’ila a yanzu za ta iya yanke shawarar abin da zai iya shiga ko fita daga cikin yankin, in ji Afirka ta Kudu, wacce lauyoyinta suka yi nuni da cewa Falasdinawa ba za su iya tserewa daga Rafah ba, yankin daya tilo da yaki bai lalata ba.

Kasar Afirka ta Kudu ta kuma nemi alkalan kotun da su ba da umarnin cewa ‘yan jarida da masu bincike na kasa da kasa su samu shiga yankin Falasdinu, lamarin da Isra’ila ta ki amincewa da shi tun ranar 7 ga watan Oktoba da fara yakin.

Har yanzu dai alkalan ba su yanke hukunci kan batun ba, Sai dai a karshen watan Janairu, sun yi kiyasin cewa, akwai hadarin gaske na kisan kare dangi a kan Falasdinawa a Gaza.

Yakin da Isra’ila ke yi a Gaza ya sa Afirka ta Kudu ta shigar da kara a kan gwamnatin kasar a watan Disambar 2023.

Afirka ta Kudu ta ce ayyukan da Isra’ila ke yi a Gaza ” kisan kare dangi ne.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments