a wata tattaunawa ta musamman da jaridar Washington Post, Fira Ministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ya bayyana cewa, Furucin jami’an gwamnatin Amurka shi ne dalilin farko na rugujewar dangantakarta da Nijar, bayan da wani babban jami’in Amurka ya yi barazana ga mahukuntan kasar a wani yunƙuri na ƙarshe game da kasancewar sojojin Amurka a kasar.
Zeine ya tabbatar da cewa dangantakar Nijar da Amurka ta tabarbare matuka, sakamakon yunkurin jami’an Amurka na yin katsalandan a cikin kulla kawance da Nijar take yi da wasu kasashen ketare, ba ya ga gaza samar da kwararan hujjoji na jibge sojojin Amurka a cikin kasar, wanda yanzu ake shirin kawo karshensa nan da watanni masu zuwa.
A ranar 10 ga watan Afrilu ne rukunin farko na masu ba da shawara na Rasha 100 suka isa Nijar tare da na’urorin tsaron sararin samaniya bayan tattaunawa tsakanin shugaban mulkin soja Janar Abdourahamane Tiani da shugaban Rasha Vladimir Putin.
Yanzu haka dai Rashawa Masu bad a shawara suna zama a sansanin sojojin saman Nijar da ke kusa da filin jirgin saman Yamai, wanda kuma ke dauke da sojojin Amurka sama da 1,000 da aka tura a shekarar 2012 domin yaki da ta’addanci a yammacin yankin Sahel na Afirka.