Firai Ministan Kasar Libya Ya Bada Sanarwan Mutuwar Babban Hafsan Sojojin Kasar

Firay ministan kasar Libya Abdul Hamid Beidah ya tabbatar da labarin mutuwar babban kwamandan sojojin kasar a gwamnatin yammacin kasar Libya Muhammad Ali Ahmad Al-Haddad

Firay ministan kasar Libya Abdul Hamid Beidah ya tabbatar da labarin mutuwar babban kwamandan sojojin kasar a gwamnatin yammacin kasar Libya Muhammad Ali Ahmad Al-Haddad da wasu mutane 4 tare da shi a hatsarin jirgin sama da ya samesu a kasar Turkiyya a lokacinda suke kan hanyarsu ta dawowa Tripoli a daren talatan da ta gabata.

Shafin yanar gizo na labarai ArabNews na kasar Saudiya ya nakalto Firay ministan yana fadar haka a shafinsa na Facebook ya kuma bayyana mutuwarsu a matsayin babban rashi ga kasar Libya. Majiyar gwamnatin kasar ta Libya ta kara da cewa an daina jin duriyar jirgin mintuna 30 bayan ya tashi daga tashar jiragen sama na Ankara babban birnin kasar Turkiyya dauke da babban kwamandan sojojin da kuma abokan tafiyarsa.

Labarin ya kara da cewa jirgin saman haya samfurin Falcon 50 ya tashi da Al-Haddad da misalin karfe 9 saura minti 8 na daren talata da nufin birnin Tripoli, amma bayan mintoci 30 jirgin ya aike da sakon saukar gaggawa kusa da garin Haymana kilomita 74 daga Ankara babban birnin kasar Turkiyya, amma daga nan an bar jin duriyarsa kwata-kwata.

Kasar Turkiyya dai tana taimakawa kasar Libya kan al-amura da dama wadanda suka hada da siyasa da tattalin arziki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted