Fira Ministan Malaysia ya jaddada cewa: Duk wata tattaunawa da ba ta magance cin zarafin da Amurka da Isra’ila suka yi wa Iran ba ta da ma’ana
Fira Ministan Malaysiya Anwar Ibrahim ya yi ikirarin cewa: “Duk wata tattaunawa game da hare-haren da aka kai wa Iran, ba tare da magance harin farko da Amurka da kungiyar ‘yan Sahayoniyya suka kai kan Iran ba, za ta zama mara ma’ana kuma tsagwaron munafunci ne.”
Kamfanin dillancin labaran “IRNA” na kasar Iran ya ruwaito cewa: Fira Ministan Malaysiya, a wata hira ta musamman da kafar NDTV a gefen taron kungiyar BRICS a birnin New Delhi na kasar Indiya, ya bayyana cewa: Kasashe da yawa ba sa son amincewa da ainihin musabbabin rikicin.
Ibrahim ya kara da cewa: “Abin da ake kira ‘rikici’ da Iran ya samo asali ne daga harin farko da Amurka ta kai tare da hadin gwiwar Haramtacciyar kasar Isra’ila, duk da haka kasashe da yawa suna gujewa amincewa da wannan gaskiyar.”
Fira Ministan Malaysiya ya kuma jaddada wajibcin kawo karshen tashin hankalin da kuma kafa adalci, yana mai cewa: “Idan ana son tabbatar da hangen nesa na mafita ta lumana, kawo karshen tashin hankalin yana da matukar muhimmanci, amma dole ne a cimma adalci; in ba haka ba, za a fada cikin tarkon munafunci da sabani.”