Majaliysar Asibirti a yankin gaza ta bayyana cewa a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakanin hamas da isra’ila a kalla falasdinawa guda 6 sun yi shahada wasu da dama kuma sun jikkata biyo bayan hari da HKI ta kaddamar a yankin Gaza
Kamfanin dillancin labarai na falasdinawa WAFa ya nakalto cewa wani bafalasdine guda yayi shahada yayin da wasu da dama kuma suka jikata a yammacin jiya Asabar bayan da jirgin sama mara matuki na isra’ila ya kai hari a al-sabra dake makwabtaka da yankin zirin gaza, a wani bangare kuma wasu falasdinawa guda biyu sun yi shahada a wani hari da isra’ila ta kai kan rufin wani gida a layin al-aqsa a yankin tel hawa dake makwabtaka da kudu maso yammacin zirin gaza
Wannan mataki yazo na kwana daya bayan da shugaban Amurka Donald trump ya sanar da cimma matsaya na abin da ya kira bord of peace da zai bada damar shiga bangare na biyu na yarjejeniyar da aka cimma na dakatar da bude wuta
kungiyar hamas ta ce za ta ajiye makamanta saboda ceto yankin Gaza amma bayan isra’ila ta dakatare da hare-haren da take kai wa, kuma ta janye daga yankin baki daya kammar yadda aka cimma a yarjejeniyar da aka kulla.