Rahotanni daga Gaza sun ambaci cewa Falasdinawa 4 ne suka yi shahada daga cikinsu har da dan sanda, yayin da wasu da dama sun jikkata, sanadiyyar hare-haren da sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kai a yankuna daban-daban a safiyar Juma’a.
Majiyar asibitocin yankin na Gaza ta ce a yankin ‘al-mawasi’ dake gundumar Khan-Yunus ne sojojin mamayar su ka kai hare-haren na yau a daidai lokacin da mutanen yankin suke yin sahur.
Ita kuwa ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu ta sanar da shahadar wani jami’in dan sanda daya wani kuma ya jikkata sanadiyyar hari da manyan bindigogi da sojojin mamaya su ka kai wani shinge na tsare a titin Salahuddin dake mashigar sansanin ‘yan hijira na “al-Buraij” a tsakiyar Gaza.
Tun bayan tsagaita wutar yaki da aka sanar a ranar 10 ga watan Oktoba na 2025, falasdinawan na Gaza ba su ga wani sauyi ba, saboda ci gaba da hare-hare da sojojin mamaya suke yi a yankin.
Daga sanar da tsagaita wutar da aka yi kuwa, adadin falasdinawan da su ka yi shahada zuwa yanzu, sun kai 618, yayin da wadanda su ka jikkata su ka kai 1663.
Amma daga 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu kuwa jumillar Falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 72,000, sai kuma wani adadin da ya kai 171, 000 da su ka jikkata, mafi yawancinsu kananan yara ne da mata. Kididdiga ta tabbtar da cewa muhimman cibiyoyin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta ruwa a yankin Gaza, sun kai 90%, da hakan ya sa ayyukan yi wa mazauna yankin mafi yawancin hidimomo su ka ta’azzara.