Kasashen Turai Sun Ca Kan ‘Yar Rahoton MDD Kan Falasdinu Francesca Albanese

Francesca Albanese, yar rahoton MDD ta musamman a kasar falasdinu da aka mamaye ta sha suka daga kasashen turai bayan wani jawabi mai zafi da tayi a birnin Doha na kasar Qatar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wata kungiya mai suna Aljazeera Org. ce ta shirya taron. Albanese ta soki HKI […]

Falasdinawa 4 Sun Yi Shahada A Lokacin Sahur Sanadiyyar Ci Gaba Hare-haren Sojojin Mamaya

Rahotanni daga Gaza sun ambaci cewa Falasdinawa 4 ne suka yi shahada daga cikinsu har da dan sanda, yayin da wasu da dama sun jikkata, sanadiyyar hare-haren da sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kai a yankuna daban-daban a safiyar Juma’a. Majiyar asibitocin yankin na Gaza ta ce a yankin ‘al-mawasi’ dake gundumar Khan-Yunus […]

‘Yan Hijira Kusan 8,000 Ne Su ka Halaka A Duniya A 2025

A kalla ‘yan hijira 8,000 ne su ka mutu da kuma bacewa a duniya a cikin shekarar 2025 da ta wuce, bisa rahoton hukumar  MDD dake kuma da ‘yan hijira. Rahoton ya bayyana ibtila’in da ya fada wa ‘yan hijrar a shekarar ta 2025 da cewa, wata babbar gajiyawa ce da duniya ta nuna. Kididdigar […]

An Kammala Tattaunawa Zagaye Na Uku Tsakanin Iran Da Amurka tare Da Samun Ci Gaba

Ministan Harkokin Wajen Oman, Badr al-Busaidi, ya sanar da kammala zagayen tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a birnin Geneva a wannan  Alhamis, tare da samun babban ci gaba. Ministan Harkokin Wajen Oman ya bayyana cewa, za a gudanar da tattaunawa a matakin kwararru a mako mai zuwa a birnin Vienna. Ya kuma tabbatar da cewa […]

Kasashen Yammacin Afirka Na Shirin Rundunar Yaki Da Ta’addanci A Yankin

Manyan Hafsoshin soji a kasashen yammacin Afirka, a wani taro da suka gudanar a birnin Freetown na ƙasar Saliyo, a wannan  Alhamis, sun jaddada mahimmancin haɗin kai tsakanin ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da ƙawancen ƙasashen Sahel a cikin shirye-shiryen su na kafa  rundunar gaggawa ta ECOWAS. Tattaunawar da shugaban ƙasar Saliyo kuma […]

Alkahira: Taron Hadin Gwiwa Tsakanin  Masar Da Sudan

Firayim Ministan Masar Mostafa Madbouly ya gana da Firayim Ministan Sudan Kamil Idris a Alkahira don tattaunawa kan ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu da kuma ba da shawara kan batutuwan da suka shafi yankin. Bangarorin biyu sun kuma tattauna abubuwan da ke faruwa a Sudan, inda Masar ta tabbatar da cikakken goyon bayanta ga haɗin kan […]