Assalamu alikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakewa tsaro da sauransu a makon da ya gabata. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
////… Madallah, masu sauraro a yau zamu fara da labara mai cewa, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya karyata labaran karya wanda kafafen yada labaran HKI suke yadawa kan cewa gwamnatin kasar Iran ta fara zartar da hukuncin kisa a kan wadanda aka kama a rikicin farkon sabon shekarar da muke ciki
Ministan Harkokin Wajen Iran ya musanta ikirarin kafofin watsa labaran ‘yan sahayoniyya, yana cewa: Ba a aiwatar da hukuncin kisa kan wani ba
Ministan yana mayar da martani ne ga karya wacce rahotannin kafafen yada labarai na ‘yan sahayoniyya suka yada kan Iran, yana mai ikirarin cewa labaran da ake yadawa ba su da inganci kuma suna da nufin amfani da karya da kauda hankalin jama’a kan al-amarin HKI da kuma biyan wasu manufofinta na siyasa.
Ministan ya rubuta a shafinsa na X a daren Laraban da ta gabata kan cewa “Lokacin da kafafen yada labarai da ke da alaƙa da Miriam Adelson wata yar siyasar HKI ta ke yada wata da’awa mai ban mamaki game da Iran, dole ne mutane su tambayi kansu wa ke amfana da wannan karya.
Araqchi ya kara da cewa: “A cikin rahotonsu na baya-bayan nan, wadannan kafafen yada labarai sun yi ikirarin cewa- awa daya kacal kafin ziyarar Netanyahu zuwa Fadar White House – cewa Iran ta ‘yaudari’ Trump.”
Araqchi ya ci gaba da cewa, saboda basa son wannan labarin ya yadu suka yada wannan labarin na kasar: “Gaskiyar magana ita ce: ba a aiwatar da hukuncin kisa kan wani a Iran ba, kuma ba a kammala shari’ar da ake wa wadanda ake tuhuma ba, banda haka an yi afawa ga fursunoni sama da 2,000, a dai dai lokacinda kasar take cika shekaru 47 da sanarar juyin juya hali a kasar”
Ministan Harkokin Wajen ya jaddada cewa: “Kafin a amince da labarin da ake yadawa, akwai bukatar a yi la’akari da wanda ke amfana da shi – da kuma wanda ke aikata yaudara.”
Araqchi Ya Ce: Iran Ta Dogara Ne Da Allah da kuma Al’ummarta Don Haka Zata Kare Musu Hakkokinsu
Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada cewa: Sun dogara daAllah da kuma al’ummarsu kuma ba za su yi watsi da hakkokinsu ba
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Haƙƙoƙin mutanen Iran da mutuncinsu ba abin sulhu ne ba, yana mai jaddada jajircewar Jamhuriyar Musulunci kan ikonta da kuma dogaro da jama’arta wajen fuskantar duk wani barazana da matsin lamba daga waje.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X, Araqchi ya rubuta cewa: “Miliyoyin Iraniyawa sun fito kan tituna a ranar Laraban da ta gabata don bikin cikan shekaru 47 na abin da masana suka kira ‘babban juyin juya hali na ƙarshen ƙarni na 20 wanda ya faru a kasar Iran.'”
Ministan Harkokin Wajen ya ƙara da cewa: “A cikin shekaru da dama tun bayan juyin juya halin Musulunci, musamman a cikin watanni goma sha biyu da suka gabata, abubuwa da dama sun faru a kasar. A cikin shekara guda kacal, mutanen Iran sun kasance waɗanda gwamnatoci biyu masu makaman nukiliya suka kai musu hare-haren da ba’a taɓa ganin irinsu ba, sai kuma wani aikin ta’addanci mafi muni a kan kasar wanda ba ko wace kasashe a duniya ne zata jurewa hakan ba, amma duk da haka, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ci gaba da kasancewa a tsaye kan kafafunta.”
Araqchi ya ci gaba da cewa: “Wannan tsayin daka ya samo asali ne daga dogaro da Allah da kuma mutanen kasar, ba kan ƙasashen waje ‘yan yaudara ba.”
Dr Larijani Ya Tattauna Da Shugabannin Kungiyar Hamas A Birnin Doha Na Qatar
A tattauna tsakanin Dr Larijani da shuwagabannin Kungiyar Hamas a birnin Doha kan al-amuran yankin Asiya ta yamma.
Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Dr Ali Larijani, ya gana da wasu shugabannin kungiyar Hamas a birnin Doha na kasar Qatar, domin sabin sabbin ci gaban da ala sami a harkokin siyasa a yankin, musamman hare-haren da HKI ke ci gaba da kai wa a yankin Gaza.
Taron, wanda aka gudanar a yammacin Laraba a Ofishin Jakadancin Iran da ke Doha, ya tattauna halin da ake ciki, isar da kayakin jin kai zuwa yankin Gaza, hanyoyin da za a karfafa tsagaita budewa juna wuta, sannan ya sake jaddada goyon bayan Iran ga manufofin Falasdinawa a yayin da ake ci gaba da samun karuwar hare-haren HKI a kansu.
A bangarenta kungiyar Hamas ba bayyana cewa a taron, Shugaban Majalisar jagorancin kungiyar, Muhammad Darwish da tawagar shuwagabannin kungiyar sun gana da Sakataren Majalisar koli ta Tsaron Kasa ta Iran, Dr Ali Larijani, a birnin Doha babban birnin kasar Qatar inda suka tabo sabbin ci gaban da aka samu a harkokin siyasa a yankin da kuma ci gaba da kai hare-haren da HKI take kai wa kan yankin Gaza.
Darwish ya gabatar da wani takaitaccen bayani game da yanayin da ake ciki a yankin da kuma jin kai a yankin Gaza, inda ya nuna ci gaba da aikata laifukan da gwamnatin HKI ke aikatawa kan al’ummar Falasdinu da kuma saba wa sharuddan yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Ya jaddada jajircewar kungiyar Hamas wajen aiwatar da yarjejeniyar da kuma hana komawa yaki.
Shugaban Kungiyar Hamas Ya Karyata labarin da ke cewa ta Cimma Matsaya Kan mika Makamanta ga makiya.
Shugaban kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Babu wata shawara da aka yanke na karbe makaman ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa.
Wani jami’in Kungiyar Hamas Osama Hamdan ya bayyana sanya Fira Ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda Kotun hukunta manya-manyan Laifuka ta Duniya ICC ke nema ruwa a jallo, “Majalisar Zaman Lafiya” wanda Shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi, “wasan kwaikwayo ne da zaman lafiya a kasar Falasdinu da aka mamaye.
Hamdan ya tabbatar da cewa; Gwagwarmaya ta kasance halaltacciyar haƙƙi ga al’ummar Falasɗinu muddin mamaya ta ci gaba, kuma ya musanta cewa ƙungiyar ta sami duk wasu shawarwari na hukuma game da kwance damarar makaman kungiyar.
A cikin sanarwar da kafafen yana labarai suka watsa a ranar Laraba da yamma, Hamdan ya jaddada kin amincewa da duk samuwar wani soje daga waje a Zirin Gaza, ya kara da cewa duk wani tallafi na ƙasa da ƙasa ya kamata ya kasance aikin ta kawai, don kare fararen hula da hana kai hare-haren HKI kan Falasdinawa. Hamdan ya ƙara da cewa Hamas ba ta sami wani daftarin shawarwari a hukumance daga masu shiga tsakani game da makaman ‘yan gwagwarmaya ba. Ya jaddada cewa: Matsayin Hamas dangane rashin mika makamanta mai ƙarfi ne, kuma ba ta amince da wata shawara a hukumance game da karbe makamanta ba, yana mai la’akari da gwagwarmaya a matsayin halaltacciyar haƙƙin Falasdinawa, muddin mamaya tana nan.
Batun Shirin makamai masu linzami na kasar Iran ba zai taba kasancewa a kan teburin tattaunawa da makiya ba
Mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci kan al-amuran tsaro, a nan kasar Iran, ya ce makaman masu linzami na Iran jan layi ne a wajen gwamnatin Iran wanda bazata amince a tsallaka shi ba, don haka ba za ta taba sanya su a kan teburin tattaunawa da makiya ba.
Rear Admiral Ali Shamkhani, ya bayyana hakan ne a gefen tattakin tunawa da zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci da aka gudanar a ranar Laraba a nan birnin Tehra.
Wannan bayanin ya zo ne a dai dai lokacinda Washington take ci gaba da matsa lamba kan fadada tattaunawar nukiliya da ake ci gaba da yi da Iran, zuwa ga batun karfin makamai masu linzami na kasar.
Kalaman Shamkhani martani ne kai tsaye ga sabbin kiraye-kiraye daga gwamnatin Donald Trump na kasar Amurka na ganin an takaita nisan makaman Iran masu linzami ta yanda basu kai kan HKI ba, ko kuma wurare masu muhimmanci na Amurka a yankin asia ta yamma.
Shamkhani ya gargadi Amurka game da farmawa kasar Iran da yaki, sannan ya kara da cewa duk wani hari a kan kasar za’a dauke shi a matsayin kaddamar da yaki.
Ya ce hanya daya tilo da za a bi don ci gaba da “tattaunawa mai inganci” ita ce a daina farfaganda” saboda a kaucewa abinda zai jefa yankin cikin tashin hankali.
Wannan bayyanin na sa ya zo ne a lokacin ziyarar da Fira Ministan HKI Benjamin Netanyahu yake yi a Washington.
Netanyahu dai na matsa lamba wa Amurka kan cewa kada ta yarda ta cimma wata yarjejeniya da Iran a tattaunawar da suke, sai idan ta kunshi takaita yawa da kuma tazarar makamanta masu linzami.
‘Yan Tawayen Sudan Sun Kai Hare-hare Kan Rumbunan Kayan Agaji a yankin Darfur
Gwamnatin Sudan ta sanar da cewa: An kai hari kan rumbunan ajiyar kayakin agaji, a dai dai lokacinda kasashen duniya da kuma kungiyoyin agaji suke nuna damuwarsu dangane da karancin abinci a kasar ta Sudan musamman a yankunan da take fafatawa da yan tawaye.
Rahotonni sun bayyana cewa: Amfani da jiragen sama marasa matuki a yankin Kordofan da ke kudu maso yammacin Sudan ya kara yawa, sannan wurga al’ummar yankin cikin hatsari.
Kanfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bada labarin cewa yara biyu sun rasa rayukansu, sannan wasu kuma suka jikkata a wani harin da yan tawaye suka kai kan wata makarantar addini a birnin Al-Rahad na yankin Kordofan ta Arewa, har ila yau da wani da wani harin da suka kai a wani rumbun ajiyar kayan abinci na Hukumar Abinci ta Duniya FAW da ke garin Kadugli. Kafin haka dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin kan cewa za a fuskanci mummunan matsalar jin kai a yankin Darfur na kasar Sudan idan hare-hare kan fararen hula sun kara yawaita a yankin.
Yara da dama sun mutu kuma wasu sun jikkata a wani hari da jiragen sama wadanda ake sarrafasu daga nesa suka kai kan wata makarantar addini a Al-Rahad, dake Jihar Kordofan ta Arewa, a hare-haren da ake suka danganta da Rundunar ‘Rapid Support Forces (RSF) ta Dakarun Kai Daukin Gaggawa na kasar ta sudan wacce ta zama yan tawaye.