Duniyarmu A Yau: Bukukuwan Nisfus Shaaban A Jamkaran

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau, shiri wanda ya ke kawo maku labarai

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau, shiri wanda ya ke kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa, tattalin arziki, zamantakewa tsaro da sauransu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///…Madallah, masu sauraro zamu fara shirimmu na yau da labarin gagarumin bukukuwan zagayowar ranar haihuwar Limami Na 12 A Masalacin Jamkaran da ke birnin Qom na tsakiyar jmi.

A daren Laraban da ta gabata ce wato daren 15 ga watan Shaaban na shekara ta 1447 hijira aka gudanar da gagarumin bikin haihuwar limami na 12 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Allah (s) wato Mohammad dan Hassan Al-askari wanda aka fi saninsa da Imam Mahdi a birnin Qum na ilmi dake kudancin birnin Tehran a nan JMI.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa taron na qom shi ne mafi girma tun bayan nasaral Juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran shekaru 47 da suka gabata. Sannan taron na bana yana cewa ne a dai dai lokacinda jiragen yakin Amura suke kawanya da JMI da nufin tumbuketa.

Imam Mahdi(a) dai shi limami na 12 daga limamai masu tsarki wadanda manzon Allah (s) ya sanyasu a matsayin khalifofinsa a bayansa har duniya ta nade. Na farkosu Aliyu dan Abitalib (a) sannan yayansa daga diyar manzon Allah (s) Fatima (s) sai kuma yayan Hussain guda 9 na karshensu shi ne Imam Mahdi (a). Kuma shi ne wanda Allah yayi alkawalin ciki duniya da adalci bayan cikarta da zalunci a karshen duniya.

A cikin musulmi dai mabiya mazhabar Shia mai limamai 12 ne da wasu tsirarun musulmi ne  kawai suka yi Imani da haihuwarsa a ranar 15 ga watan Shaaban shekara ta 255 bayan hijira, wanda ya nuna a halin yanzu yana da shekaru kusan 1200 a duniya.

Da fatan Allah ya gaggauta bayyanarsa don kubutar da bil’adama daga musifun da suka fada ciki a hannun azzaluman shuwagabannin duniya.

Iran Ta Kara Karfin Garkuwan Makamanta samfurin Ballistic Bayan Kara Kyautatasu

Wani babban sojan JMI ya bayyana cewa kasar ta kara kyutata karfin garkuwan makamai masu linzami samfurin ballistic na kasar a dai dai lokacinda take fuskantar barazanar sojojin Amurka zasu farwa kasar da yaki.

Tashar talabijan ta Prestv a nan Tehran ta nakalto manjo Janar Abdurrahin Musawi, yana bada wannan sanarwan ne a jiya Lababa a lokacinda ya je ziyarci daya daga cikin garuruwan makamai masu linzami na JMI karkashin dakarun juyin juya halin musulunci na kasar Iran wato IRGC.

Janar Musawi ya bayana cewa bayan yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka dorawa JMI, dakarun IRGC sun kara kyuatta makamansu masu linzami samfurin billistic ta yadda yana iya zama garkuwa da kuma mai kai farmaki .

A wannan ziyar dai Manjo Janar Musawi ya sami rakiyar Burgedia Janar Majid musawi kwamandan sojojin IRGC mai kula da sararin samania (Aerospace Force). Daga karshe ya tabbatar da cewa dakarun IRGC a shirye suke su fuskanci dukkan barazanar makiya. Musamman irin wanda ya kashe Iraniyawa 1,064 a cikin watan Yunin shekara ta 2025. Inda makaman Amurka da HKI suka cilla suka kashe manya manyan kwamandojin sojojin JMI wadanda suka hada da shaid Janar Hussain Salami, da Shahid janar bakiri da shahid Janar Hajji zadeh, da kwamnadan dakarun IRGC ta khatamul anbiyai da ke nan Tehran.

Iran: Wawtar Kasar Jamus Ce ta Fidda Ita Daga Taka Rawa A Tattaunawar Shirin Nukliyar Kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa wawtan waziri ko shugaban gwamnatin kasar Jamus ne ya fidda kasar daga cikin tattaunawa dangane da shirin Nukliyar kasar Iran.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Abbas Aragchi yana fadar haka a shafinsa na X a safiyar yau Alhamis ya kuma kara da cewa, a cikin watan satumban shekarar da ta gabata ce kasashen turai guda uku da ake kira Trico a takaice wato Faransa da Jamusa da kuma burtania, suka janye daga tattaunawar shirin nukliyar kasar Iran karkashin matsin lamba na wazirin kasar ta Jamus  Friedrich Merz, sannan suka shigar da bukatar a sake dorawa JMI takunkuman tattalin arziki na MDD kan kasar Iran wadanda suka shafi shirin ta na makamashin Nukliya.

Ministan yana maida martani ne ga Merz bayan ya rubuta a shafinsa na X yana cewa yana son ya kara takurawa kasar Iran ya kuma shiga tattaunawa cikin shirinta na makamashin Nukliya don ya gaggauta kawo karshensa.

Aragchi ya ce wawtar da yayi a baya ne yasa yake nadamar matakan da suka dauka kan kasar Iran a lokacin. Banda Jamus a kwai wasu kasashen yamma da dama da suka nuna rashin iya siyasa wanda ya zama masu musiba daga baya.

Sai gashi a halin yanzu Merz yana roko a sake maida shi cikin tattaunawar don ya cimma wasu manufofinsa.

Tehran

Mataimakin kwamandan rudnunar soja ta “Khatamul-Anbiya” Kanar Miyomars Haydari,ya yi gargadi akan cewa; Duk wani hari da za a kawo wa kasar Iran, zai fuskanci mayar da martani mai tsanani, sannan kuma ya kara da cewa; Babu yadda za a iya tabbatar da tsaro a cikin wannan yankin ba tare da Iran  tana da tsaron ba.

Haka nan kuma ya ce, taba tsaron Iran, yana nufin cewa babu wani wuri da zai zama mai aminci da zaman lafiya ga Amurka da kuma Isra’ila da kawayensu a cikin wannan yankin.

Dangane da yadda Amurka ta girke makamanta a cikin wannan yankin, mataimakin kwamandan rundunar ta ” Khatamul-Anbia” ya ce; babban kuskuren lissafi ne, idan kuwa har hakan ya ci gaba, to abinda zai sami Amurka shi ne shan kashi da zai tilasta mata ficewa daga yankin.

A jiya Laraba ne dai Rasha ta sanar da cewa daga yanzu ba za ta ci gaba da aiki da yarjejeniyar kayyada makaman Nukiliya da ta kulla tsakaninta da Amurka ” Neo Start”, bayan da wa’adinta ya zo karshe a yau Alhamis.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha wacce ta fitar da wata sanarwa a jiya Larabar, ta ce; Muna kirdaron cewa  bai zama wajibi ba bangarorin da suke a karkashin yarjejeniyar Nukiliya ta ” Neo Start” su yi aiki da ita ba,amma duk da haka za mu yi aiki cikin sanin ya kamata dangane da abinda ya shafi Nukiliya.

Kasashen na Rasha da Amurka dai sun kulla yarjejeniyar kayyade yawan makaman Nukiliya ne a 2010, ta yadda yawan wuraren harba makaman da kowace kasa za ta mallaka ba zai wuce 800 ba, kuma su kansu manyan makaman Nukiliyar na kowa kar ya wuce 1,550.

Haka nan kuma bangarorin biyu sun amince da a rika gudanar da bincike domin tabbatar da abinda yake faruwa a kasa.

A gefen Amurka, har yanzu ba ta fitar da wata sanarwa ba akan zuwa karshen wa’adin yarjejeniyar ta kayyade makaman Nukiliya a tsakaninta da Rasha.

Ministan harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce; A halin yanzu babu wata sanarwa da zai yi, yana mai kara da cewa; A nan gaba  Shugaban kasar ta Amurka Donald Trump zai yi Magana akai.

Kasar China ta yi gargadi akan kare wa’adin yarjejeniyar tana mai cewa duniya za ta shiga cikin wani yanayi wanda ya fi na baya hatsari.                Shi kuwa Paparoma Leo na 14 ya yi kira ne da kar a koma gasar kera makamai, sannan kuma bukaci ganin an yi aiki da kyawawan halaye da bil’adama ya yi tarayya da juna akai,maimakon ci gaba da rayuwa a cikin tsoro.

HKI Ta Dakatar Da Fitar Da Marasa Lafiya Daga Gaza Zuwa Jinya A Kasashen Waje

Majiyar kungiyar Red Crecen ta Falasdinawa ta bada sanarwan cewa a jiya Laraba HKI ta dakatar da shirin fitar da marasa lafiya da suke gaza don jinya a kasashen waje ta kofar shiga yankin da ke rafah ba tare da bada wani dalili ba.

Rashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Raed Al-Nems kakakin kungiyar kungiyar bada agaji ta Red Cresen yana fadar haka a jiya, ya kuma bayyana cewa ya sami labarin ne daga hukumar lafiya ta duniya wacce ta fara shirin fitar da Falasdinawa marasa lafiya a Gaza tun bayan da yahudawan suka bude kofar Rafa.

Yahudawan sahyoniyya sun bada wannan sanarwan ne a dai dai lokacinda suka kai mummunan hare-hare kan falasdinawa a gaza a jiyan. Labarin ya kara da cewa mai yuwa su sake bude kofar ta Rafah a yau Alhamis don ci gaba da fitar da Falasdinawa wadanda suke matukar bukatar jinya a kasashen waje. Saboda babu kayakin aikin a asbitin Al-Amal da ke Khan Yunus na yankin Gaza.

Amuli Larijani: Imam Khomaini (a) Ya Bude Wata Sabuwar Kofa A Falsafar Siyasar A Duniya

Shugaban majalisar ‘Masalahar Tsarin musulunci’ a nan kasar Iran Aya. Amuli Larijani ya bayyana cewa Imam ruhullahil Khumaini (a) ya budewa duniya wata kofa ta falsafar siyasa da democradiyyar addini, wacce aka ginata da goyon bayan mutane ga gwamnatin addini a Iran.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Amuli Larijani yana fadar haka a safiyar yau a lokacinda ya jagoranci majalisarsa zuwa hubbaren Imam khomai (a) dake kudancin birnin Tehran don jaddada bai’a gareshi da kuma siyasarsa.

Aya. Larijani ya kara da cewa Imam Khomaini (a) ya gabatar da siyasar democdiyyar addinine a dai lokacinda kowa a duniya yana ganin tsarin damocradiyya ta kasashen yama ta cika duniya zalunci, wanda ya bayyana a fili mai karfi ne yake yin abinda ya ga dama a duniya.

Daga karshe babban malafiya ya bayyan Imam Khomam Khimaini(a) da kuma Magajinsa Imam Khaminaei a matsayin abin buga misali a sanin addinin musulunci da falsafansa da kuma tsoron Allah a wannan zamanin. Mutanene wadanda suka san addinindu kuma suka san zamaninsu.Shugaban majalisar ‘Masalahar Tsarin musulunci’ a nan kasar Iran Aya. Amuli Larijani ya bayyana cewa Imam ruhullahil Khumaini (a) ya budewa duniya wata kofa ta falsafar siyasa da democradiyyar addini, wacce aka ginata da goyon bayan mutane ga gwamnatin addini a Iran.

Aya. Larijani ya kara da cewa Imam Khomaini (a) ya gabatar da siyasar democdiyyar addinine a dai lokacinda kowa a duniya yana ganin tsarin damocradiyya ta kasashen yama ta cika duniya zalunci, wanda ya bayyana a fili mai karfi ne yake yin abinda ya ga dama a duniya.

Shugaban majalisar maslahar tsarin musulunci a kasar Iran yace, tsarin democradiyya ta kasashen yamma ta maida doniyar ‘rayuwar daji’ mai karfi ya cinye marasa karfi.

Daga karshe babban malafiya ya bayyan Imam Khomam Khimaini(a) da kuma Magajinsa Imam Khaminaei a matsayin abin buga misali a sanin addinin musulunci da falsafansa da kuma tsoron Allah a wannan zamanin. Mutanene wadanda suka san addinindu kuma suka san zamaninsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted