Duniyarmu A Yau: Amurka Ta Tsara Kifar Da JMI A Matakai 7

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa zamantakewa tattalin arziki da kuma tsaro. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

////…Madallah, masu sauraro labarinmu na farko yana cewa, gwamnatin Iran shiga neman fasahar makamashin nukliya gadan-gadan ne bayan shigowar HKI, da kuma barnan da yi mata, a farko farkon shirinta na neman mallakar fasahar.

Shugaban Hukumar makamashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Islami ya bayyana cewa shishigin HKI da kuma barnan da ta yiwa kasar Iran suna daga cikin abubuwan da suka tilastawa hukumarsa ta bukaci kwarewa a harkokin fasahar Nukliya da kuma tashe makamashin Uranium da kanta, ba tare da dogaro da wata kasa a duniya ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Islami yana fadar haka a wani taro a jiya Laraba a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa. Wannan ne ya tilastawa gwamnatin kasar kafa hukumar makamashin Nukliya mai zaman kanta, duk da cewa samun fasahar yana da matukar sarkakiya, hakama kayakin aikin sarrafa makamashin yuranium duka basa da saukin samu, saboda HKI da kasashen yamma ne suka fi korewa a wannan fannin a lokacinda kuma su suke da kayakin aikin.

Yace, wannan ya tilastawa kasar da farko samarwa, bincike, gwaji, da ginawa, samar da kayakin aikid da kuma fitar da sakamakon da ake bukata. Daga nan ne kasashen yamma musamman Amurka suka kuduri anniyar raba mutanen kasar Iran da wannan fasahar, Amurka ta fada a fili, ko ta lalata wannan fasahar ta hanyar diblomasiyya ko kuma tare da amfani da karfi. Wanda ya zuwa yanzu ta yi amfani da dukkan wadan nan hanyoyi ta kasa kaiwa ga manufarta.

Banda kashe gomomin masana fasahar nukliya na kasar wanda HKI da Amurka suka yi a watan yulin shekara ta 2025 Amurka ta yi amfani da karfin don lalata cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar ta Iran, sai dai duk da cewa sun lalata wani bangare na wadan nan cibiyoyi amma sun kasa hana kasar ci gaba da amfani da wannan fasahar.

IRGC ta ce, tace Maikiya JMI Sun Tsara Matakai har 7 don kifar Da JMI A Rikici Na watan jenerun wannan shekara.  

Shugaban bangaren leken asiri na rundunar kare juyin juya halin musulunci Burgedia Janar Majid Khademi ya bayyana cewa makiya JMI sun tsara matakai har guda 7 a rikicin yan ta’adda ta Daesh a farkon wannan shekara a kasar, kuma manufarsu ta karshe ita ce tumbuke gwamnatin JMI.

Khademi ya bayyana haka ne a jiya Laraba a hirar da yayi da kafafen yada labarai a kasar. Ya kuma kara da cewa, Amurka da HKI duk sun tsare kan cewa da farko zasu fara tada zanga-zanga a cikin gida, sannan su a hankali su fara kawo hare-hare, kamar yadda suka yi a cikin yakin kwanaki 12 a cikin watan Yulin shekara ta 2025.

Yace sun bukaci yan ta’adda da magoya bayansu su kai hare hare kan sansanin sojojin kasar da barikokin sojojin kasar da sauran jami’an tsaro don su raunanasu, sannan su kuma zasu shigo da yaki ta sama da kasa don daga karshe ganin bayan JMI.

Sannan sun yi kokarin yada karya kan  yawan mutanen da aka kashe a rikicin su dorawa JMI alhakin kashesu su kuma halattawa kansu shigowa da yaki kan kasar Iran tare da sunan kubutar da mutanen kasar daga gwamnatin JMI ta Iran.

Yace gwamnatocin makiya sun kai hare-hare ta yanar gizo don lalata sadarwa da kuma ayyukan khidimomin mutane a kasar amma duk wannan bai kaisu ga nasara ba.

Ministan harkokin cikin gida na HKI ya Bukaci gwamnatin kasar ta samayar da yanayin da falasdinawa zasu Kwarara Zuwa Wajen Kasar su Da Aka Mamaye.

Ministan harkokin cikin gida na HKI Bezalel Smotrich  ya yi kira ga gwamnatin kasar ta kodaitar ta kuma yi dukkan abinda zata yi don ganin Falasdinawa da kansu su fara kwarara zuwa wajen kasarsu da aka mamaye saboda bawa HKI fadada kasar zuwa dukkan yankunan kasar Falasdinu da suka mamaye, sannan don kuma debe fatan kafa kasar Falasdinu nan gaba.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Smotrich yana fadar haka a ranar Talatan da ta gabata, wa majalisar gudanarwa na ta jam’iyyar Sahyoniyya ta addini a wani wuri kusa da birnin Ramallah.

Har’ila yau  Smotrich ya bukaci gwamnatin HKI ta kawo karshen a hukumance ga yarjeniyar Oslo ta shekara 1990 da falasdinawa wanda yake maganar warware matsalolin da ke tsakaninta da Falasdinawa cikin ruwan sanyi.

Taron na jam’iyyar sahyoniyya masu kishin addini dai shi shirin tabbatar da ikon gwamnatin su kan dukkan kasar Falasdinu nan da shekara ta 2030. Ya bukaci korar Falasdinawa daga kasar Falasdinu daga Gaza da kuma abinda ya kira lardin ‘ Judea and Samaria’ wanda yake nufin yankin yamma da kogin Jordan.

Pakistan Ta Kashe Yan Ta’adda 12 A Yankin Bajaur Sannan Ta Rasa Sojoji 11

Majiyar   sojojin kasar Pakistan ta bayyana cewa sojojin sun kasha yan ta’adda 12 a wani harin da suka kai kansu a wani shingen da suka kafa a garin Bajaur a yayinda suka rasa sojoji 11 a ranar litinin da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, sojojin kasar ta Pakistan sun sha alwashin murkushe yan ta’adda wadanda tace suke samun goyon baya daga kasashen waje. Labarin ya kara da cewa hare-haren ranar 16 ga watan fabrayru a zo ne a dai dai lokacinda gamayyar Jami’an tsaron kasar suke aikin tabbatar da tsaro a garin na Bajaur, wanda ya sami maida martani mai tsanani daga sojoji da kuma sauran jami’an tsaro.

Wannan ya faru ne kafin yan ta’addan su tada bom mai karfi wanda ya lalata ginin da Jami’an tsaron suke amfani da shi da kuma wasu gine-ginen gidajen mutanen gari da suke kusa da shi.

Banda haka wata yarinya guda ta rasa ranta a yayinda wasu da dama suka ji rauni. Daga ciki har da mata da yara.

Rahoton ISPR na sojojin kasar ta Pakistan ta kamala da cewa yanta’addan wadanda suke samun goyon bayan kasar Indiya ana kiransu ‘Fitna Al-Khawarij’. Kuma kasar Pakistan zata kawar da su kwatakwata daga yankin.

A nan Iran, an Ga Jinjirin Watan Ramadan ne a daren ranar Laraba, inda  Ranar Alhamis Daya Ga Watan Ramadan.

Hukuma mai kula da ganin jinjirin wata karkashin ofishin jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran ta tabbara da cewa an ga jinjirin watan Ramadan a daren Jiya Laraba wanda ya maida watan Shaaban 29 sannan ranar Alhamis ta zama daya ga watan Ramadan mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto hukumar tana fadar haka a daren jiya Laraba bayan sun sami rahoton ganin watan daga tawagoji da dama da suka yi aikin ganin watan na cewa an ga watan. A wasu kasashen Musulmi dai an fara azumin watan Ramadan tun jiya Laraba.

Shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan ya karfafa mahangar jagoran juyin juya halin musulunci dangane da tattaunawar da ke gudana a tsakanin Iran da Amurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya, ya kuma yi watsa da tattaunawa don kawai tattaunawar kanta ba tare da fatan za’a kai ga wata natija ko sakamako abinda amincewa tsakanin kasashen biyu ba.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa, ana gudanar da tattaunawa tsakanin kasashen biyu ne tare da  amincewar Jagoran juyin juya hali Imam Sayyid Aliyul Khaminaei. Ya ce manufarmu itace warware matsaloli da rashin fahintar da ke tsakanin bangarorin biyu, ba tattaunawa don mujarradin tattaunawa ba.

A jiya talata ce aka gudanar da zagaye na biyu na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya a birnin Geneva na kasar Swissland. Kuma bayan taron tawagar Iraniyawa ta bayyana cewa an sami ci gaba amma kafin a dora akwai bukatar ko wani bangare ya sake tuntubar kasashensu don fayyace matsayinsu a kan wasu al-amura.

Amurka dai tana bukatar Tehran ta amince a tattauna kan makamanta masu linzami da siyasarta a gabas ta tsakiya da kuma shirinta na makamashin Nukliya. Amma Iran ta ki amincewa sai kan shirinta na makamashin Nukliya, sannan shi ma tare da amincewa zata tashe makamashin a cikin gida gwargwadon bukatarta.

A wani jawabinda ya gabatar a Jiya Jagoran Juyin juya halin musulunci ya bayyana cewa da Alamun Amurka tana son mamayar kasar Iran, amma mutanen Iran ba irin mutanen da za’a mamaye kasarsu ba. Kamar yadda Hussain (a) ba zai taba yiwa Yazid mubaya’a ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted