Jim kadan da a nan Tehran aka sanar da shahadar shugaban bangaren siyasa na kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas, kasashen duniya sun fara mayar da martani.
Kasar China ta bakin ma’aikatar harkokin wajenta ta yi tir da kisan gillar da HKI ta yi wa shugagaban ofishin siyasa na kungiyar ta Hamas,, tana mai kara da cewa; Wannan irin danyen aikin zai iya jefa wannan yankin da ma duniya cikin Karin rikici da rashin zaman lafiya.
Ita ma kasar Rasha ta fitar da tata sanarwar da a ciki ta bayyana cewa: “Kisa ne na siyasa wanda ko kadan ba abinda za a lamunta da sh ba ne.”
Shi kuwa mataimakin shugaban Majalisar tarayyar Rasha Konstantin Kosachev ya aike da wani sako da a ciki yake cewa; Kisan da aka yi wa Isma’ila Haniyyah, zai hada kan dukkanin kungiyoyin da suke fada da HKI.
Kasar Qatar ta hanyar ma’aikatar harkokin wajenta, ta yi Allawadai da kisan da HKI ta yi Isma’ila Haniyyah, tare da cewa; Abinda ya faru laifi ne babba da HKI ta aikata, kamar yadda ta saba kai wa fararen hula hari.
Haka nan kuma ta ce; Kisan na Isma’ila Haniyyah, zai sake jefa Gaza da kuma wannan yankin na yammacin Asiya cikin rikici da rashin zaman lafiya. Fira ministan kasar Lebanon Najib Mikati yana cikin wadanda su ka yi tir da kisan tare da cewa,lamari ne mai hatsari