Dubban masu Zanga-zangar da su ka hada da yahudawa da Amurka sun yi hadu ne a birnin Washinton a jiya Laraba, inda suka nuna kin amincewa da duk ziyarar Fira Ministan HKI zuwa wannan kasa.
Masu Zanga-zangar dai sun rika bayar da taken ‘yantar da Falasdinu’ da yin tir da kisan kiyashin da HKI take yi wa Falasdinawa.
Jami’an ‘yan sanda sun killace yankin da masu Zanga-zangar su ka taru da hana su shiga cikin ginin “Capitol Hill”.
A jiya da dare ma dai wasu daruruwan yahudawa masu Zanga-zangar sun taru inda su ka yi zaman dirshan a gaban ginin majalisar dokokin Amurka a matsayin cewa ba da sunansu Isra’ila take tafka laifi ba.