Dubban Falasdinawa Sun Fito Zanga Zangar Tunawa Da Ranar Naqaba ko Musiba

Dubban falasdina mazauna yankin yamma da kogin Jordan ne suka fito zanga zangar tunawa da ranar Nakaba, ko kuma musiba ta shekara 1948, a lokacinda

Dubban falasdina mazauna yankin yamma da kogin Jordan ne suka fito zanga zangar tunawa da ranar Nakaba, ko kuma musiba ta shekara 1948, a lokacinda aka shelanta kafuwar HKI a kan kasar Falasdinu da aka mamaye.

Kamfanin dillancin labaran Isna na kasar Iran ya bayyana cewa a ranar 15 ga watan Mayun shekara 1948 ne aka shelanta kafuwar HKI a kan kasar Falasdinu wanda turawan Ingila yan mulkin mallaka suka mamaye tun bayar yakin duniya na biyu.

Falasdinawa suna tunawa da wannan ranar ne a ko wace shekara tare da fatan wata rana zasu koma kasar su daga inda aka koresu daga shekara ta 1948 da kuma musibun da suka biyu baya.

Kungiyar Falasdinawa yan gudun hijira sun bayyana cewa babu abin zai maye gurbin gurinsu na komawa kasarsu da kuma gidajensu da ake koresu.

Ranar nakba ta wannan shekarar, wato shekaru 76 da faruwan sa a dai lolacinda sojojin HKI suka kasha falasdinawa kimani 35,000 a gaza a cikin watanni 7 da suka gabata, da kuma raunawa wasu falasdinawa 78,000.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments