Dubban ‘yan Tunisia ne suka fito zanga-zangar lumana a babban birnin kasar kan abin da suka kira rashin adalci da danniya na wannan gwamnatin, yayin da suke zargin Shugaba Kais Saied da mulkin kama karya.
Zanga-zangar ta kasance wani babban al’amari ne a baya-bayan nan da ya mamaye wasu bangarori a kasar wanda ya shafi ‘yan jarida, likitoci, bankuna, bangaren sufuri da sauran ababen more rayuwa.
A watan da ya gabata, wasu fitattun kungiyoyin kare hakkin dan adam suka sanar da cewa hukumomi sun dakatar da ayyukansu saboda zargin suna karbar tallafin kudi daga wasu kasashen waje.
Amnesty International ta ce murkushe kungiyoyin kare hakkin jama’a a kasar yana bukatar kawo dauki, yayin da gwamnati ke ci gaba da kama wa da tsare mutane ba bisa ka’ida ba, kwace kadarori, takaita ayyukan bankuna da dakatar da su a wasu lokutan ma da kai hari kan kungiyoyi masu zaman kansu, wannan abin damuwa ne matuka.