Search
Close this search box.

Rikici Tsakanin Sojojin Sudan Da Dakarun Kai Daukin Gaggawa Ya Lashe Rayukan Fararen Hula

Kazamin fada tsakanin sojojin Sudan da Dakarun kai daukin gaggawan kasar ya janyo hasarar rayuka da raunata mutane masu yawa a birnin Al- Fasher fadar

Kazamin fada tsakanin sojojin Sudan da Dakarun kai daukin gaggawan kasar ya janyo hasarar rayuka da raunata mutane masu yawa a birnin Al- Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa

Wata kungiyar kasa da kasa ta sanar da cewa: An samu mace-macen mutane da kuma jikkatan wasu da dama, baya ga raba wasu iyalai fiye da 1,500 da matsugunansu a birnin Al Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa da ke yammacin kasar Sudan, sakamakon fadace-fadace da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin sojojin Sudan da Dakarun kai daukin gaggawa na rundunar Rapid Support Forces ta kasar.

Majiyoyin cikin gida sun bayyana cewa: Jiragen saman yakin sojin Sudan sun kaddamar da wasu jerin hare-hare a wasu sansanonin Dakarun kai daukin gaggawa da suke cikin birnin, inda majiyar sojojin ta kara da cewa: Sojojin Sudan sun gudanar da aikin tallafa wa runduna ta shida da ke birnin El Fasher, kuma mayakan dakarun kai daukin gaggawa na Rapid support Forces sun yi luguden wuta da jiragen sama masu saukar ungulu kan yankunan tsakiyar birnin El-Fasher da wasu yankunan da suke arewaci da kuma kudanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments