Dakarun Yemen sun kai hare-hare kan jiragen ruwan Isra’ila, Amurka da Birtaniya

Dakarun Yaman sun sanar da kaddamar da hare-hare guda hudu kan jiragen ruwa na gwamnatin Isra’ila, da Amurka da Birtaniya, wadanda dakarun na Yemen suka

Dakarun Yaman sun sanar da kaddamar da hare-hare guda hudu kan jiragen ruwa na gwamnatin Isra’ila, da Amurka da Birtaniya, wadanda dakarun na Yemen suka yi wa farmakin lakabi da  “Trio of Evil.”

Kakakin rundunar sojin gwamnatin san’a Birgediya Janar Yahya Saree ne ya sanar da ayyukan farmakin  a cikin wata sanarwa da ya fitar.

“An aiwatar da aikin na farko ne da makamai masu linzami da dama da suka nufi jirgin ruwan Isra’ila mai suna MSC Unific a cikin Tekun Arabiya, inda suka isa kan jirgin kai tsaye ba tare da wani tarnaki ba. in ji shi.

Kakakin ya ce “An aiwatar da farmakin  na biyu ne da makamai masu linzami na ballistic da na cruise, wanda aka kadddamar a kan jirgin ruwan dakon mai na Amurka Delonix a cikin tekun Bahar Maliya a karo na biyu a wannan makon.”

Harin na uku an kai shi ne kan jirgin ruwan Burtaniya mai suna Anvil Point a Tekun Indiya, in ji Saree, inda yace an yi amfani da makamai masu linzami da dama wajen kaddamar da harin, wanda kuma dukkansu sun sami jirgin ruwan kai tsaye.

A farmaki na hudu kuma dakarun na Yemen sun kai harin ne a kan wani jirgin ruwa mai suna Lucky Sailor a cikin tekun Bahar Rum.

Saree ya ce an kaddamar da farmakin ne domin nuna goyon baya ga Falasdinawa a zirin Gaza, wadanda ke fama da yakin kisan kare dangi na Isra’ila.

Har ila yau kuma hakan na  nufin mayar da martani ne ga hare-haren da Amurka da Birtaniya ke kai wa kan al’ummar kasar Yemen , a matsayin yunkurin dakatar da ayyukansu na goyon bayan Falasdinu, in ji Saree.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments