Dakarun Sojin Kasar Yamen Sun Sanar Da Haramtawa Jiragen Ruwan HKI  Zirga-Zirga A Tekun Maliya

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar yamen sun sanar cewa za su dauki mataken soji kan muradun HKI a yankin baki daya, kuma zai

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar yamen sun sanar cewa za su dauki mataken soji kan muradun HKI a yankin baki daya, kuma zai hada kai hare-hare da makamai masu linzami, kuma sun haramatawa jiragen ruwan Isra’ila motsi a fadin tekun bahar maliya,

haka zalika rundunar sojin ta ce ayyukan soji za su ci gaba da karuwa gwagwardon yadda sojojin HKI suke mayar da martani na hare hare da za’a kai musu, kuma za su ci gaba da bude wuta gwargwadon yadda rikicin yake ci gaba da karuwa.

Kuma sun jaddada matsayinsu na ci gaba da riko da mataken da suke dauka na yaki da makiya Amurka da Isra’ila kuma ta jadda cewa ba za ta dakatar da kai hare-harenta ba matukar aka ci gaba da yin kawanya da daukar mataken soji.

Daga karshe ya bayyana cewa mataken soji da za su dauka zai ci gaba da wanzuwa matukar makiya an ci gaba da kai hare hare, kuma wannan yana zuwa ne sakamakon taurin kai da gwamnatin sahyuniya take nunawa na ci gaba da tafka laifukan yaki kan Alummar falasdinu da kuma keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakaninta da kasar labanon

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted